*Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida: Tunji-Ojo na aiwatar da ƙudurin Tinubu na Ajandar Sabon Fata*

*Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida: Tunji-Ojo na aiwatar da ƙudurin Tinubu na Ajandar Sabon Fata*

*Tunji Ojo, ya shiga ofishinsa da ƙafar dama:*

A tsarin dimokuraɗiyya, kyakkyawan fata shi ne abin da kowace sabuwar gwamnati kan bai wa ‘yan ƙasa. Samar da nagartaccen shugabanci ta hanyar yi wa jama’a alƙawari da cikawa don samar da abubuwan da a baya aka rasa su. Sai dai kuma a wasu lokutan, burin al’umma ba ya cika a ƙarshen lamari saboda rashin nagarta, ba daga ɓangaren zaɓaɓbun shugabanni ba kaɗai har ma da waɗanda aka naɗa don taimaka wa zaɓaɓbun shugabanni wajen sauke nauyin gwamnati da ya rataya a wuyansu.

A ɓangare mai zaman kansa, ta la’akari da ma’aikata ana iya gane irin jajirtattun masu gidan da ake da su a wuri, walau ko dai ya kasance manaja ko jami’in sanya ido. Ma’ana, a matsayinka na shugaba, waɗanda ka kwasa don su yi aiki a ƙarƙashinka za su yi tasiri wajen nasarorin da za ka cimma, haka dai al’amarin yake walau a ɓangare mai zaman kansa ko a ɓangaren gwamnati.

Zuwan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin Shugaban Tarayyar Najeriya da taken “Sabon Fata” tunani ne mai kyau ga ƙasa wadda ta kasa samun nagartaccen shugabanci a tsakanin shekaru masu yawa da suka shuɗe.

Zuwan Tinubu da taken “Sabon Fata” bai zo da mamaki ba ga waɗanda suka kasance suna bibiyar tsarin shugabancinsa na gomman shekaru da suka shuɗe ba tare da son zuciya ba. Idan da akwai wani abin kokwanton cikin lamarinsa, bai wuci na shin su wa da wa zai ɗauko don su taya shi aiki wajen cimma ƙudirinsa ba. Amma kuma da shugaba irin Tinubu, haɗa tawagar da za su yi aiki tare shi ya fi komai sauƙi a gare shi.

Ga Shugaban da ya yi harka da ɓangare mai zaman kansa kafin ya shiga siyasa, ana sa ran waɗanda zai kamo hannayensu don su zo su taya shi aiki dole ya zamana masu tunani ne irin nasa kuma sun yi harkoki irin nasa a baya kafin daga bisani su tsunduma cikin siyasa.

Ya isa hujja naɗin da Tinubu ya yi wa Honorabul Bunmi Tunji Ojo, ƙwararre a ɓangaren fasahar sadarwa (ICT), kuma matashin da ke ajin ‘yan shekara 40, wanda ya yi harka da manyan hukumomi irin su Bankin Duniya da Kamfanin Fetur na Ƙasa (NNPC) da Hukumar JAMB da NCDMB da sauransu masu yawan gaske, wanda har yau ana cin moriyar wasu ayyukansa. A matsayin wanda ya tsaya da ƙafafunsa, ya shiga harkar siyasa ne don sadaukarwa wajen cigaban al’umma.

Matasan Najeriya masu rajin cigaban ƙasa da al’ummarta da tabbatar da nagartaccen shugabanci ba za su taɓa mancewa da wannan karamcin da Shugaba Tinubu ya yi musu ba da naɗin da ya yi Bunmi Tunji Ojo a matsayin Ministan Harkokin Cikin Gida. Wanda hakan ke nuni da akwai buƙatar magabata su yi aiki tare da matasa don amfanin ƙasa, godiya muke Ya Shugaban Ƙasa.

Dalilan miƙa godiyarmu ba sai an je da nisa ba, tuni aka rantsar da Honorabul Bunmi Tunji Ojo tare da wasu 44 a matsayin ministoci a ranar a 21 ga August, 2023, inda aka damƙa masa Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida wadda ke da haƙƙin kula da harkokin tsaron cikin gida, bai wa ‘yan Najeriya shaidar zama ɗan ƙasa, bai wa ‘yan ƙasa izinin kasuwanci, haɗa da sanya ido a hukumomin kula da sha’anin shige da fice da ta tsaron farin kaya da ta kula da gidajen yari da sauransu.

Idan muka ɗauki Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa, sanannen al’amari ne wannan hukumar tana ƙarkashin kulawar Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ne wadda aka ɗora wa alhakin kula da iyakokin ƙasa da bai wa ‘yan ƙasa fasfo (passport) na ƙasa da ƙasa, ma’aikata ce wadda shekaru da dama tana fama matuƙa wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta. Kalaman Ministan a lokacin da ya karɓi ragamar jagorancin ma’aikatar inda ya ce, “Na zo ne don in yi aiki”, wannan manuniya ce kan cewa yana da masaniya game da matsalolin da suka addabi ma’aikatar da kuma yaƙinin zai maganance su.

Baya ga shan alwashin kammala samar da fasfo (passport) sama da dubu 200 da ke jibge a ofishin hukumar, nan take ya sunkuya aiki inda a cikin ƙasa da makonni uku da kama aiki, Honorabul Bunmi Tunji Ojo ya kammala fasfo dubu 160 daga cikin sama da dubu 200 da ke jibge a ofishin hukumar.

A gare mu, wannan nasarar abar a yaba ce, kuma muna yin haka ne domin ƙarfafa wa Ministan da tawagarsa gwiwa a bakin aiki don ci gaba da kyakkyawan aikin da suka fara don amfanin ‘yan Najeriya. Kuma ko ana ha maza, ha mata, ba za su yi ƙasa a gwiwa ba.

Kazalika, mun yi wannan ne domin ƙalubalantar sauran ministocin don kowannensu ya miƙe ya yi aikin da ke gabansa ba tare da wani jinkiri ba.

Saboda G.K Nelson ya faɗa cewa, “Jama’ar da suka yi nasara ba wai wata baiwa ce ta musamman ba, jajircewa suka yi suka yi aiki.”

Mun yaba wa Ministan da salon shugabanci nagarin da ya nuna ta hanyar aiki tuƙuru, inda ya ba da lokacinsa ba dare, ba rana wajen aiwatar da harkokinsa tare da tawagarsa domin sauya labarin ma’aikatarsa zuwa mai daɗi

Gamayyar ƙungiyoyi masu rajin a yi aiki da gaskiya, muna fata wa’adin wannan gwamnatin ya zama lokacin ɗaukaka ga Najeriya musamman ga matasa da dattawa, maza da mata, talaka da mai kuɗi, mazauna birni da karkara, gwamnati da masu zaman kansu da sauransu.

Muna kyautata zaton wannan gwamnatin ta samar da cigaba mai nagarta ga ɗaukacin ‘yan Najeriya ba tare la’akari da bambancin yare, ko addini, ko al’ada ba, cigaba wadda za ta game Arewa da Kudancin ƙasa baki ɗaya.

Sai dai, ya zama wajibi masoyan Najeriya su yi amannar cewa, idan muna buƙatar Najeriya ta zauna a mazaunin da ya fi dacewa da ita a tsakanin ƙasashen duniya, dole a haɗa kai a yi aiki tare, dole mu yi watsi da abubuwan da suke haifar da rarrabuwar kai a tsakaninmu, dole kowane ɗan ƙasa ya daina kallon akwai bambanci a tsakaninsa da ɗan uwansa.

Yayin da nake shirin kammala wannan bayanin, bari in gabatar mana da kalmomin hikima daga John Donne, inda yake cewa: “Mafificin shugaba da na sani, shi ne mai kallon nasara ba ta samuwa sai an haɗa kai, sannan a zaɓo masu nagarta a tsakaninsu waɗanda a ƙarshe su ne za su jagoranci sauran jama’a zuwa ga nasara. Abin da ya fi burgewa shi ne, su ɗin nan da aka zaɓo, sukan nemi a tallafa musu kuma ba su ƙin taimako. Shugabanni na ƙwarai sun kwana da sanin cewa su kaɗai ba za su iya ba, kuma ko da mafi ƙarfi a cikin jama’a shi ma yana buƙatar a tallafa masa.”

Bisa la’akari da waɗannan kalmomi na sama, muna kira ga ɗaukacin masu ruwa da tsaki a Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida da ma wajen ma’aiktar da a mara wa ƙudurin cigaban da Minista Ojo ke da shi. Haka nan, muna kira ga ‘yan jarida da sauransu da su mara wa Ministan baya ta hanyar yaɗa rahotanni game da kyawawan ayyukansa don cigaba ma’aikatarsa da ma ƙasa baki ɗaya.

*****
*Kwamred Haruna Abdulsalam, shi ne Daraktan Tsare-tsare na Gamayyar Ƙungiyoyi Masu Rajin Cigaban Al’umma da Shugabanci Nagari (COCTA), ya rubuto ne daga Abuja*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *