AN ZO WAJEN – Gwamna A.A Sule zai bincike badakalar Al-makura 

AN ZO WAJEN – Gwamna A.A Sule zai bincike badakalar Al-makura

Daga Zubairu Lawal
Masu iya magana kance maida Takobi ranar fada tsorone. Hakanan wasu na cewa idan Kaduna tayi atishawa Nijariya zata kamu da mura. Masu hangen nesa na cewa duk abinda aka shuka watarana zai yi tsiro.
Gwmnatin Abdullahi Sule ta jihar Nasarawa ta kudduri aniyar bincikar badakalar da tsohuwar Gwamnatin Umar Tanko Al-makura ta aikata a cikin jihar Nasarawa.
Gwamnatin Abdullahi Sule tare da Majalisan dokokin jihar Nasarawa sun bankado tsohuwar cinikayyar kaddarorin da tsohon Gwamnan ya sai da.
Majalisan dokokin jihar Nasarawa karkashin jagorancin kakakin Majalisan Balarabe Abdullahi ta kafa kwamitin da zasu gudanar da binciken badakalar sai da kaddarorin Gwmnatin da Umar Tanko Al-makura yayi a lokacin da yake Gwamnan jihar a shekarar 2017.
Kakakin Majalisan dokokin jihar Hon. Balarabe Abdullahi ya bayyana kuddurin da shugaban masu rinjaye na Majalisan Hon.Muhammad Adamu Omadefu ya gabatar kan batun a zauren Majalisa.
Tuni kakakin Majalisan ya bayyana samar da kwamitin mutum Tara da zasu bincike yadda aka sayar da kaddarorin jihar Nasarawa dake birnin Lagos da Kaduna da Jos.
Ya bukaci kwamitin ta gaggauta gudanar da bincike da kuma yadda aka saida da inda kudin suka Shiga.
Kakakin Majalisan ya nada Hon Larry Ven Bawa a matsayin Shugaban kwamitin.
Sauran mutanin sun hada da Hon Iliya Luka Zhekaba, da Hon Musa Ibrahim, Sakataren kwamitin Hon Mohammed Omadefu, Hon Suleiman Azara, Hon Danladi Jatau, Hon Saidu Gude, Hon Mohammed Isimbabi, Hon Mohammed Oyanki
Majalisan dokokin jihar Nasarawa ta bukaci kwamitin ta tabbatar ta gudanar da aikin bisa ga kwarewa.
Al-umman jihar Nasarawa na kallon wannan matakin da Gwamnatin Abdullahi Sule ta dauka baya rasa nassaba da sabanin da ya Dade yana ruruwa a kasa tsakanin Gwamnan da uban gidansa.
Wasu na ganin yanzu anzo karshen inda za ayi baram baram tsakani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *