Muna goyon bayan Gwamna Sule ya daukaka kara – Aliyu Bello
Daga Zubairu Lawal
Jam’iyyar APC mai Mulki a jihar Nasarawa ta goyi bayan Gwamna Abdullahi Sule da ya daukaka kara a kotun zabe na gaba.
Da yake zantawa da Manema Labarai ranar Laraba a shalkwatar Jam’iyyar dake garin Lafia Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Nasarawa Alhaji Aliyu Bello.
yace; dukkan Shugabannin Jam’iyyar APC na kananan hukumomi da Shugabannin dake mulki a kananan Hukumomi ya’yan Jam’iyyar sun amince Gwamna Abdullahi Sule ya garzaya zuwa kotun daukaka kara domin kalubalantar hukuncin kotun sauraron karar zabe da ta ayyana Dan takarar PDP a matsayin Wanda yayi nasara a zaben Gwamna da aka gudanar ranar 18 /2/2023.
Alhaji Aliyu Bello yace; Jam’iyyar APC bata amince da wannan hukuncin ba domin cike yake da son zuciya.
Yace; Alkalai biyu da suka ayyana Dan takarar Jam’iyyar PDP David Emmanuel Ombugadu a matsayin Wanda yayi nasara Jam’iyyar APC bata gamsu da hujjojin da sukayi amfani da shi ba.
Tace; Alkali daya da ya bayyana Gwamna Abdullahi Sule a matsayin Wanda yayi nasara shine yayi hukuncin da ya dace kuma ya kawo hujjojin da suka dace da hankali.
Shugabannin Jam’iyyar APC ya qara da cewa Membobin Jam’iyyar PDP suna zuwa gidajen mutanin APC suna cimasu mutumci bai kamata ba.
Suna kira garesu dasu dai na, idan zasuyi farin ciki bai kamata suna cin zarafin wasu daba Jam’iyyarsu daya ba.
Yayi kira ga hukuma data dauki mataki kada abin ya wuce gona da iri, domin baasu amince ana fakewa da murna ana cin zarafinsu ba.
Alhaji Aliyu Bello yayi godiya ga Gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago da suka sulhunta ba tare da zuwa yajin aiki ba.
Yace; wannan nasarace ga al’umman Nijariya.