Babban burina  ceto rayuwar yara kanana su samu ingantaccen ilumi. -Inji Darda’u Mairafi

Babban burina  ceto rayuwar yara kanana su samu ingantaccen ilumi.
-Inji Darda’u Mairafi
Daga Zubairu Lawal 
Shugaban Makarantar Mairafi Darda’u  Academic. mai baiwa Gwamna Abdullahi Sule Shawara. Kuma Chairman Fittiyanun Islamic a Karamar Hukumar Lafia cikin jihar Nasarawa Alhaji Muhammad Noma Darda’u Mairafi.
Ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema Labarai a bikin bude sabon makarantar da ya gina a Unguwar Farin Kasa cikin garin Lafia.
Yace ; Na gina  wannan makaranta domin ceto rayuwar Ilumin yara kanana kamar yadda Mahaifina yakeyi.

mahaifinmu tsarin rayuwarsa kenan shi ya fara kafa makarantar Islamiyya hade da boko a fadin garin lafia  domin samar da ilumin yara kanana.

Yadda Mahaifinmu ya tafiyar da wannan tsarin na taimakawa domin samar da Ilumi da tarbiya cikin al’ummanmu abin yana bani sha’awa tun ina karami.
Ban gina wannan makarantar domin tsauwalawa ga al’umma ba. Gani nayi duk fadin unguwan nan babu fitaccen makarantar kwara daya da yara zasuyi karatu. Yara suna wasa a unguwa ko yaushe, shiyasa na yanke Shawara gina makaranta anan duk da cewa ni ba mazaunin unguwar bane.
Kuma komai cikin sauki muka tsarashi duk da cewa  ingantaccen nakarantane, amma kudin shiga dana suturar makaranta da komai N14,000 ne.
Nan unguwane na talakawa suna bukatar taimako. Shiyasa naga ya dace na taimaka da makaranta mu sanya kudi kadan domin iyaye su iya biya.
Makarantane na kowa da kowa Musulmi da Kirista, haka tsarin yake. Idan aka tashi Boko sai Islamiyya su shiga.
Babban burine na ceto rayuwar yara kanana su samu ingantaccen ilumi. Ina da kuddurin samar da Asibiti a wannan unguwar kusa da makaranta. Domin al’umma su samu gurin shan magani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *