Yan APC sun gudanar da zanga zangar goyon bayan Gwamna sule a Lafia

Yan APC sun gudanar da zanga zangar goyon bayan Gwamna sule a Lafia

Daga Zubairu Lawal
Ya’yan Jam’iyyar APC sun gudanar da zanga zangar nuna goyon bayansu ga Gwamna Abdullahi Sule kan nuna rashin amincewa da shari’ar Kotun sauraron karar zabe.
Masu zanga zangar da suka hada maza da mata sun gudanar da zanga zangar ne daga Shataletalen zuwa Sakatariyar jam’iyyar APC dake titin shanda cikin garin Lafia.
Masu zanga zangar suna rera wakokin nuna goyon bayansu da Gwamna Abdullahi Sule, da kuma nisanta kansu da kin yarda da hukuncin da kotun sauraron karar zabe ta yanke a zamanta na ranar 2/10/2023.
Da yake jawabi ga masu zanga zangar Shugaban jam’iyyar APC na jihar Nasarawa Alhaji Aliyu Bello yayi godiya ga masu zanga zangar. Ya kuma nuna goyon bayan jam’iyyar da wannan sallon da membobin ta suka dauka na gudanar da zanga zangar lumana.
Shugaban jam’iyyar yace; jam’iyyar APC bata amince da wannan hukunci ba. Tana kalubalantar hukuncin kotun.
Yace; jam’iyyar APC ta amince da daukaka kara da Gwamna Abdullahi Sule zaiyi. Yace; a wannan shari’ar alkalai ukune biyu sun nuna jam’iyyar PDP ce tayi nasara daya yace APC ce tayi nasara.
Yace; a kotun gaba akwai alkalai biyar sune zasuyi hukunci. A kotun koli akwai alkalai bakwai. Yace; shari’a yanzu aka fara. Yayi kira ga masu zanga zangar dasu kwantar da hankalinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *