kashi 80 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar mashako ba su yi allurar rigakafi ba -Dr Faisal Shu’aibu

kashi 80 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar mashako ba su yi allurar rigakafi ba -Dr Faisal Shu’aibu

Gwamnatin tarayya ta ce kaso 97 cikin 100 na mutanen da suka kamu da cutar mashako da akafisani da Diphtheria a Najeriya sun fito ne daga jihohi biyar na arewa.

Babban Daraktan Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko na  kasa, Dr Faisal Shuaib ne bayyana haka a wata ziyarar aiki domin duba matakan da ake dauka na yaki da barkewar cutar mashako a jihar Kano, ya ce jihohin su ne Kano da Yobe da Borno da Katsina da kuma Kaduna.

Dr Faisal wanda ya ziyarci cibiyar kula da masu fama da cutar mashako dake asibitin kwrarru na Murtala Muhammed a Kano, ya ce bayanai sun nuna sama da kashi 80 cikin 100 na wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar da kuma wadanda suka mutu ba su yi allurar rigakafi ba. .

Ya yi tsokaci kai tsaye kan labaran karya da game da alluran rigakafi, kamar yadda aka yada jita-jita akan cewa rigakafin polio yana haifar da rashin haihuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *