Zaman lafiyan da Hadin kan al’umman Nasarawa ke gabanmu ba siyasan addini ba – Shugaban Matasan PDP

Hadin kan al’umman Nasarawa da zaman lafiya ya damemu ba siyasn addini ba
Shugaban Matasan PDP
Daga Zubairu Lawal
Shugaban gamayyar kungiyar matasa daga Jam’iyyar PDP yayi kira ga al’umman jihar Nasarawa masamman yan siyasa dasu daina alakanta siyasa da addini.
Gungun matasan sunyi wannan kirane yayi hira da manema Labarai a Sakatariyar yan Jaridu a birnin Lafia cikin jihar Nasarawa .
Shugaban gamayyar Kungiyar matasa na jam’iyyar PDP a jihar Nasarawa Kwamared Daniel Agbo.yace; bai kamata yan siyasa dake jihar sunayiwa juna yarfe da sunan siyasan addini ba.
Yace; dukkanin bangarorin siyasu na jihar na amfani da wannan damar domin kushe jam’iyyar da suke adawa da ita.
Yace; duk cikan jam’iyyar babu Wanda aka kafata da addini. Kwamared Daniel Agbo yayi kira ga masu sukar Gwamna Abdullahi Sule da cewa ba asalin Dan jihar Nasarawa bane, yazone daga jihar Borno wannan ba dai dai bane. Gwamna Abdullahi Sule cikakken Dan jihar Nasarawa ne, Wanda yake da iko na zama komai a jihar Nasarawa.
Yace; batanci da yarfe ba zai amfanemu da komai ba. Face ya haifar da rigima a tsakaninmu. Yayi kira ga dukkan bangarorin siyasa dasu rikayin abinda zai haifar da zaman lafiya da kaunar juna.
Yace; yan PDP dake murna da hukumcin da kotu tayi. suyi murna cikin natsuwa da tsari banda cin zarafin abokan adawa. Suma masu bakin ciki da hukuncin da kotu yayi suyi bakin cikinsu banda cin zarafin wani.
Shugaban gamayyar kungiyar matasan PDP yace; duk bangarorin siyasan biyu sun fake da nuna yarfe na addini, da nuna cewa alkalan da sukayi hukuncin sun nuna addinanci. guda biyu Kirista suka zabe Hon Devid Emmanuel Ombugadu na Jam’iyyar PDP. Guda daya Musulmi ya zabe Gwamna Abdullahi Sule na Jam’iyyar APC.
Yace; wadan nan kalamai basu dace da al’umman jihar Nasarawa ba.
Burin al’umman jihar Nasarawa shine samar da zaman lafiya da hadin kan al’umman jihar baki daya.
Daga karshe yayi kira ga jami’an tsaro da manyan yan siyasan jihar da sarakuna da duk mai fada aji dasu shiga cikin lamarin a kawo karshen wannan mummunar siyasan batanci da batun addini.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *