Jam’iyyar APC ta kalubalanci Dattawan PDP a Nasarawa

Jam’iyyar APC ta kalubalanci Dattawan PDP a Nasarawa

Daga Zubairu .Lawal
A wani taron manema labarai da ta kira ranar Laraba 18/10/2023 a Sakatariyal Jam’iyyar APC a cikin garin Lafia domin mai da martani kan maganganun da jam’iyyar adawa ta PDP tayi a kafafen sadarwaZ ta kasa
Shugaban Jam’iyyar APC a jihar Nasarawa Alhaji Aliyu Bello ya kalubalanci dattawar Jam’iyyar PDP na jihar dan gane da wani sunayen da suka kira kansu.
Shugaban Jam’iyyar APCn yace; Tsohon Shugaban kwamitin amintattu na Jam’iyyar PDP Sanata Wali Jibir a taron manema labarai shi da Arch.Jafar Ibrahim Muhammad sun danganta kansu da cewa Dattawan Musulman PDP.
Yace; wannan sakin layine a harka siyasa tunda take bai tabajin ance cikin Jam’iyyar siyasa akwai bangaren Musulmai ko Kiristoci ba Sai a jihar Nasarawa.
Bello yace. Su dai Jam’iyyar APC uwa daya uba daya suke babu musulmai babu kirista sunansu ya’yan APC.
Shugaban Jam’iyyar APC ya kara da cewa sun amince kotun sauraron karar ta baiwa Dantakarar Jam’iyyar PDP David Ombugadu nasara. To amma ai akwai kotun daukaka kara da kuma kotun Allah ya’isa. Dan haka Sai kowa ya bari yaga abinda zai faru a gaba da gaban gaba.
Shugaban APC yayi kira ga masu zantukar batanci a yanar gizo da su daina domin babu wani cigaba da zai haifar face tashin hankali.
Yace; Babban burinmu zaman lafiyan jihar Nasarawa dan haka kowa yayi hakuri ya bar kotu tayi hukuncinta.
Aliyu Bello yace; Jam’iyyar PDP tana gudanar da taron manema labarai tana cin zarafi ga Gwamnatin Injiniya Abdullahi Sule da jam’iyyar APC.
Yace; tun bayan hukuncin da kotun sauraron karar zabe tayi Jam’iyyar APC tayi shuru. Amma Jam’iyyar PDP kullun sai surutai sukeyi sun fadin karya da maganganu na cin zarafi da takala.
Yace; Jam’iyyar PDP tana cewa bamu daukaka kara ba, ina ruwansu da ko mu daukaka kara ko kar mu daukaka.kara?
Sannan ya zargi kakakin yada labarai na Dan takarar Gwamna a Jam’iyyar PDP Dr. Mike Omeri game da maganganu kan Gwamnatin Abdullahi Sule da kuma zantukar tada zaune.
Yace; PDP da Dan takararta David Emmanuel Ombugadu sunayiwa tsarin Demukurdiyya zagon kasa da hawan qawara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *