Mutum biyar da zasu tafiyar da Nasarawa united sun fara aiki

Mutum biyar da zasu tafiyar da Nasarawa united sun fara aiki

Daga Zubairu Lawal
Gwamnatin jihar Nasarawa ta kafa kwamitin mutum biyar da zasu jagoranci tafiyar da kungiyar kwallon kafa ta jihar Nasarawa da ake kira (Nasarawa United).
Kwamitin mutanin biyar da zasu jagoranci kungiyar wasan kwallon kafan sun hada da Dr. Othman Ibrahim Ahmed  a matsayin Shugaba. Sai Managan kungiyar kwallon kafan Mr. Solomon Babanjah. Sauran membobin kungiyar sun hada da Idris Rilwan da Musa Ahmad da Musa Usman Oruma.
Gwamnatin jihar Nasarawa ta mika masu takardan kama aiki tun a ranar 17/10/2023 ta ofishin Sakataren Gwamnatin jihar Barrister Ubandoma Aliyu.
 
Da yake zantawa da manema Labarai lokacin da suka ziyarci filin wasa na jihar Nasarawa dake Bukan-Sidi. Shugaban Kungiyar Nasarawa united Dr. Othman Ibrahim Ahmed yace; zasu hada karfi da karfe suyi aiki kansu a hade domin ganin kungiyar takai ga samun nasarar dawowa matakin buga babban wasa na rukunin Nigeria Premier Football League (NPFL).
Yace; a bara  kungiyar ta sauka zuwa gasar Nigeria National League (NNL) kuma babu wani Dan jihar da yaji dadin wannan matakin da kungiyar ta je. Amma yanzu yana da kwarin giwar kungiyar zata dawo matakinta nada, tunda yanzu kungiyar tana da kwararon yan wasa da Babban mai horarwa Kochi Adams Othman.
Yace; Gwamna Abdullahi Sule ya baiwa kungiyar da jagororinta duk wani abubuwan da suke bukata domin samun nasarar dawowa matsayinta na baya.
Haka zalika kungiyar ta gabatar da launin Rigunan da zasu amfani da su a gasar wannan kakar ta bana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *