Ina da kwarin giwa kan nasarar Lobi Stars  inji Dr. Sam Ode

Ina da kwarin giwa kan nasarar Lobi Stars

 inji Dr. Sam Ode
Daga Zubairu Lawal
Yace; Ina da kwarin giwa kungiyar Lobi Stars zatayi Nasara a wasan da zata fafata da kungiyar Abia warriors.
Mataimakin Gwamnan jihar Benue Dr. Sam Ode yace; Kungiyar Lobi Stars tana taka mahimmiyar rawa a gasar da take fafatawa a sauran wasannin da take bugawa a gasar NPFL.
Dr. Sam Ode ya bayyana hakane a lokacin da ya ziyarci filin wasa na jihar Nasarawa dake Bukan-Sidi a garin Lafia, inda kungiyar Lobi Stars ke buga wasa a matsayin gida.
Yace kwalaye biyu da kungiyar Lobi Stars ta jefa a ragar kungiyar Abia warriors Babban nasarane.
Mataimakin Gwamnan jihar Benue Dr Sam Ode ya jajantawa al’umman jihar Benue dangane da asarar rayukan da ya faru a ranar Juma’a a karamar hukumar Oturko, bayan yan fashi sun afkawa al’umma a bankuna.
Shima mai horar da yan wasa na kungiyar Lobi Stars Eugene Agagbe ya nuna jin dadinsa da nasarar da kungiyarsa ta samu.
Yace; kungiyar zata cigaba da samun nasara a gasar NPFL. Kuma yana fatan samun nasarar daukar Kofi a gasar.
Mai horar da yan wasa kungiyar Lobi Stars ya godewa al’umman jihar Nasarawa da suke basu goyon baya a duk lokacin da suke buga wasa.
Wasan da aka fafata a ranar Lahadi kungiyar Lobi Stars ta samu nasara kan kungiyar Abia warriors da ci biyu da nema.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *