Zamu farfado da Darajar wasan kwallon kafa a Nasarawa Inji Salisu Basira

Zamu farfado da Darajar wasan kwallon kafa a Nasarawa

Inji Salisu Basira
Dan takarar kujerar Shugabancin wasannin motsajiki a jihar Nasarawa ( FA Chairman) Alhaji Silisu Usman Galadiman ya bayyana kuddrinsa na maido da darajar wasannin kwallon kafa a fadin jihar Nasarawa.
Dan takarar ya bayyana hakane gaban mai martaba Sarkin Doma lokacin da yakai masa ziyara, sai dai ya samu wakilcin Fakacin Doma Alahaji Yakubu a masarautan.
Alhaji Salish Usman Galadima Wanda akewa lakabida (Basira) yace; wa Sarkin Doma burinsa na tsayawa takara shine ya taimakawa jihar Nasarawa wajen daga darajar matasa a harkan wasannin kwallon kafa da sauransu.
Yace; a jihohi anyiwa jihar Nasarawa nisa. Yau a kungiyar kwallon kafa ta Nasarawa United tawagar  dake jan ragamar kungiyar ta hanyar koyarwa,yan jihar basu wuce mutum biyar ba.
Yace; idan Allah yasa ya samu nasarar zama shugaban kula da harkokin kwallon kafa a jihar Nasarawa a kowani Karamar hukuma zai zakulo Kochawa ya biya masu kudi suje Lagos su karo Ilumin horar da yan wasa, ta inda zasu samu takardan shedar zama cikakun masu horar da yan wasa kwallon kafa.
Haka zalika yace; suma Alkalan wasa zai biya masu kudi suje Abuja ko Lagos domin samun cikaken horo na gogewa.
Da yake mai da martani a madadin Sarkin Doma Alhaji Yakubu Fakacin Doma yace; Andoma yaji wannan rokon kuma yana nuna farin ciki da sanya albarka.
Yace; kowa a jihar Nasarawa yasan Andoma da sun harkan wasannin saboda wannan dalilinne yasa aka nadashi Shugaban yan wasa kwallon kwando na jihar Nasarawa.
Baya ga fadan Sarkin Doma. A filin taro Shugabannin kula da harkokin wasanni daga kananan hukumomi, sun amince da Takarar Alhaji Salish Usman Galadima da Malam Adamu Shigabarta a matsayin Shugaba da mataimaki.
Jerin Shugabannin kananan hukumomin sun hada
1. Muhammad Sidi Lawal Keffi
2. Abimiku  Nasarawan Eggon
3. Muhammad Abdullahi Obi
4. Musa Salihu Toto
5. Usman Aliyu Adeka Doma
6. John Usman Kokona
7. Abudulmumin Nuhu Samba
8. Nasiru Na Ali Keana
9. Abubakar Gambo Awe
Wadanan Shugabannin sune masu zaben Shugaba na jihar. Kuma sun rattaba hannu gami dayin alkawarin zaben Alhaji Salish Usman Galadima a matsayin Shugaban kula da wasannin na jihar Nasarawa.
Alhaji Salish Usman Galadima ya bayyana burinsa na farfado da gasar cin cupn Kananan hukumomi da Emir’s Cup da Inter. Schools wadanda aka fara bugawa a shekarar 1996 zuwa 1998. Yace;  zai dawo da martabar buga wannan gasar domin cigaban matasa na jihar Nasarawa. Yace; yau jihar Nasarawa muna alfahari da muna da mutanin dake buga kwallon kafa a kasashen waje irin su Sunusi Ibrahim Ja’afar Babayaro.wadanda kuma duka sun samu tafiyane da taimakon Allah da taimakon Basira.
Nan take Dan takarar ya amshi koken da daluban Government College Doma sukayi masa na rashin kwallaye da Sandan rodi na tsaron raga.
Salish Usman Galadima ya ziyaci makarantar kuma ya tabbatar masu da za’akawo masu wadannan abubuwan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *