Ayyukan raya kasa kungiyar (IPAC) ta yabawa Gwamna Abdullahi Sule

Ayyukan raya kasa kungiyar (IPAC) ta yabawa Gwamna Abdullahi Sule

Daga Zubairu Lawal

Kungiyar hadaka ta jam’iyya da ake kira Inter Party Advisory Council (IPAC)  ta yabawa Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule bisa ga ayyukan raya kasa na cigaban jihar.

Da yake zantawa da manema Labarai jin kadan bayan giwayawa dan ganewa idanunsu irin ayyukan cigaba da Gwamna Abdullahi Sule ya samar a jihar Nasarawa.

Shugaban Kungiyar Alhaji Yusuf Sani Yabagi yace; hakika kungiyar ta gansu da Samar da tashar mota ta zamani mai suna Sani Abacha Buss Terminal da Gwamna Abdullahi Sule ya samar a Karamar hukumar Karu.

Yace; tashar tasamar da tsaro da dumbin ayyukanyi ga matasa maza da mata.

Ya kara da cewa kasashen da akaci gaba ana amfani da tasoshin mota na zamani irin wannane saboda rage cinkoso.

Kungiyar ta zagaya karamar hukumar karu inda ta ganewa idanunta sauran ayyukan raya kasa da Gwamna Abdullahi Sule yayi tsawan shekarun da yake mulki.

Sannan sun garzaya karamar hukumar Keffi inda suka ziyarci ofishin Shugaban Karamar hukumar Keffi da kasuwanni da kwalajin kiwon lafiya da sauransu.

Tawagar ta gangara Karamar hukumar Kokona da Akwanga domin ganin ayyukan Gwamna Abdullahi Sule a sauran yankunan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *