Gwamna Sule ya yabawa kungiyar G5 da suka shirya liyafan tayashi murna

Gwamna Sule ya yabawa kungiyar G5 da suka shirya liyafan tayashi murna
Daga Zubairu Lawal
Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya yabawa kungiyar G5 data shirya taron liyafan tayashi murna samaun nasara a kotun daukaka karar zabe.
Da yake jawabi a madadin Gwamna Abdullahi Sule, Babban Ma’aji mai kula da asusun jihar Nasarawa Hon. Musa Ahmad Baraden Nasarawa  yace wannan nasarar na al’umman jihar ne baki daya.
Yace; Gwamnan ya bayyana gamsuwar sa da cewa kotun koli zata maimaita hukuncin da kotun daukaka kara tayi ne wacce ta ayyana shi a matsayin wanda yayi nasara a zaben gwamna na ranar 18 ga watan Maris a jihar.
Gwamna Sule ya fadi haka ne a sadda yake Magana a wurin wata liyafa da wata kungiyar siyasa ta G5 ta shirya dangane da cin nasarar sa a kotun daukaka kara da ya gudana a project quarters dake nan Lafia.
Yace; wannan farin cikin ba na jam’iyyar APC kadai bane na al’umman jihar Nasarawa ne baki daya.
Ya bukaci al’umman jihar dasu cigaba da tabbatar da hadin kai da zaman lafiya domin cigaba da gudanar da ayyukan cigaba.
A nasa jawabin Shugaban Jam’iyyar APC Alhaji Aliyu Bello ya kalubalanci masu zanga zangar dake furta kalaman da bai dace ba.
Yace; kowa dan jihar Nasarawa ne, kuma shari’a kotu jeyi. Ba a gama shari’a ba.
Aliyu Bello yace; mulki na Allah ne duk Wanda Allah ya bashi ya kamata al’umman jihar su hada kai su bishi domin cigaba jihar da zaman lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *