Jam’iyyar APC tayi kira ga PDP data gargadi magoya bayanta a Nasarawa

Jam’iyyar APC tayi kira ga PDP data gargadi magoya bayanta a Nasarawa
Daga Zubairu Lawal
Shugaban Jam’iyyar APC na jihar Nasarawa Alhaji Aliyu Bello yayi kira ga Shugabannin jam’iyyar PDP dasu gargadi magoya bayansu dasu daina maganganun na batanci da zai kawo rashin hankali.
Alhaji Aliyu Bello yace; shari’a na zaben jihar Nasarawa da kotu tayi ta raba gardamane kuma akwai sauran shari’a a gaba.
Yace nasarar da Gwamna Abdullahi Sule ya samu a Kotun daukaka kara nasarace da al’umman jihar Nasarawa ne baki daya suka samu.
Yace; kalaman batabci da nuna bambamci da cewa wani dan jihar ne , wani ba dan jihar bane, bai kamata ace ana jin wannan a bakin yan siyasan PDP ba.
Yace Jam’iyyar PDP ita ta tsayar da Abdullahi Adamu kuma kabilar Apawa ne daga Garaku.
Sannan ita ta tsayar da Aliyu Akwe Doma kabilar Alago daga Doma.  CPC , APC ta tsayar da Umar Tanko Al-makura kabilar Gwandara daga Lafia.
APC ta tsayar da Abdullahi Sule kabilar Kanuri daga Akwanga. Wanene ba dan jihar Nasarawa ba.
Yace; a kotun sauraron kara anbaiwa Ombugadu nasara APC ta hakura ta daukaka kara.
A kotun daukaka kara an baiwa Abdullahi Sule na jam’iyyar APC nasara ya kamata PDP ta daukaka kara zuwa kotun kili. Amma magoya baya suna zanga zanga suna fadin kalamai na batanci da zai kawo rashin hankali a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *