Kasafin Naira Biliyon,199.9 zai buda sabon shafin ayyukan raya kasa a jihar Nasarawa -Gwamna Sule

Kasafin Naira Biliyon,199.9 zai buda sabon shafin ayyukan raya kasa a jihar Nasarawa

Daga Zubairu Lawal

A ranar Juma’a 1/12/2023 Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya kaddamar da kasafin kudi na shekarar 2024 da yakai adadin Naira Biliyon,199.9

Kasafin da Gwamna Sule ya kaddamar a zauren majalisan Dokokin jihar karkashin Jagorancin Tsohon kakakin Majalisa na rikon kwarya Hon.Abel Bala Wanda ya rike majalisan bayanda Kotun daukaka karar zabe ta watsakalar da Kakakin Majalisan Hon. Balarabe Abdullahi mai wakiltar mazaber Umasha/Ugya, a ranar Talata.

Da yake jawabi gaban Membobin Majalisan dokokin jihar, Gwamna Abdullahi Sule yace; wannan kasafin zai kawo cigaba so sai a fadin jihar Nasarawa.

Yace; kuddurin Gwamnatinsa na raya karkara da birane da samar da abubuwan more rayuwa da walwalan al’umman jihar, duk kasafin ya tanadesu.

Kasafin zai buda sabon shafi na samar da hanyoyi da bangaren ilumi da tsaro harma da bunkasa aikin gona dan cigaban al’umman jihar Nasarawa.

Guraren da zasufi samun moriyar wannan kasafin sun hada da fannin Ilumi N41.9billion,

Kiwon lafiya  Naira Biliyon.27.5. sai tsaftar muhalli Naira Biliyon 5.5, da bangaren ruwan sha Naira Biliyon 41.9. Bangaren ayyuka Naira Biliyon22.7 .

Kakakin Majalisan na rikon kwarya Hon.Abel Bala  ya yabawa Gwamnatin Abdullahi Sule kan yadda take kokari wajen samar da cigaba a jihar Nasarawa da bada kulawa ga al’umman jihar..

Bayan kaddanar da kasafin kudin ne Membobin Majalisan suka gudanar da zaben sabon kakakin Majalisan da mataimakinsa.

An zabe Hon. Dan Ladi Jatau na jam’iyyar APC daga mazaber Kokona a matsayin kakakin Majalisa.

Sannan aka zabe Hon. Muhammad Adamu Oyenki na Jam’iyyar PDP daga mazaber Doma a matsayin mataimakin Kakakin Majalisan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *