Ganduje ya karbi bakwancin tsohon mataimakin Gwamnan Nasarawa a Jam’iyyar APC

Ganduje ya karbi bakwancin tsohon mataimakin Gwamnan Nasarawa a Jam’iyyar APC

Daga Zubairu Lawal

Shugaban Jam’iyyar APC ta kasa Hon. Abdullahi Umar Ganduje ya karbi bakwancin tsohon mataimakin Gwamnan jihar Nasarawa kuma tsohon karamin Mininstan Jihohi tsohon  Sanata Hon. Solomon Ewuga zuwa Jam’iyyar APC.

Solomon Ewuga ya sauya shekane daga Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC a jihar Nasarawa ranar Asabar 6/1/2024.

Solomon Ewuga ya kasance jigo a siyasan jihar Nasarawa Wanda ya dade ana damawa da shi cikin jigajigan yan siyasa da tauraronsu ke haskawa a fadin jihar.

Da yake Jawabi a wajen taron sauya shekar a garin Lafia  Shugaban Jam’iyyar APC Hon. Abdullahi Umar Ganduje yace; kasancewar ire-iren su Solomon Ewuga cikin Jam’iyyar APC cigaban so sai ga jihar dama kasa baki daya.

Ganduje yace; irin nasarorin da Gwamnatin APC take samarwa shiyake baiwa jama’a sha’awar zuwa Jam’iyyar APC.

Ya kara da cewa ayyukan cigaba da Jam’iyyar keyi zai bata damar samun nasara a jihohin Nijariya baki daya a zabe mai zuwa.

Shima Babban Sakataren Gwamnatin Tarayya Dr. George Akume ya yabawa Gwamnan jihar Nasarawa kan ayyukan raya kasa da tattalin arziki dayake samarwa domin moriyar al’umman jihar Nasarawa.

Gwamnan Abdullahi Sule mai masaukin baki yace: ganin haske cikin tafiyar Gwamnatin APC a jihar Nasarawa ya sanaya Sanata Solomon Ewuga ya juyo zuwa Jam’iyyar APC.

Yace; Solomon Ewuga hazikin Dan siyasane dake hangen nesa. Shigowar Solomon Ewuga da sauran yan wasu Jam’iyya cikin APC zai kara tabbatar da nasarorin Gwamnatin APC a jihar.

Tsohon Gwamnan jihar Nasarawa Sanata Umar Tanko Al’makura yace: Jam’iyyar APC tayi babban nasara wajen maido da Solomon Ewuga gidansa na asali.

Yace: da Solomon Ewuga aka kafa Jam’iyyar APC a kasa sune wakilan Jam’iyyar sune sukayi tsare tsare, amma daga baya ya barta. Dawowar Solomon Ewuga abin alfaharine, yanzu ya zama tankar babu wata Jam’iyyar adawa a jihar Nasarawa.

Shima Jagoran masu sauya shekar Sanata Solomon Ewuga yayi godiya ga Shugaban Jam’iyyar APC Hon. Abdullahi Umar Ganduje da Sakataren Gwamnatin Tarayya da sauran manyan baki da suka halarci wannan taron.

Yace: APC gidansune a da kuma yanzu ya dawo. Ya bar Jam’iyyar PDP saboda babu komai da ya ragemata sai son rai da damuwa.

Shima Shugaban Jam’iyyar APC ta jihar Nasarawa Alhaji Aliyu Bello ya yabawa Solomon Ewuga da sauran da sauka sauya shekar. Yace sunyi dogon tunani kuma sunyi amfani da damarsu wajen ganin an tafi tare wajen gina jihar Nasarawa, a matsayin tsintsiya madaurinki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *