Gwamnatin Nasarawa ta baiwa Ilumi mahimmanci a kasafin kudi na 2024

Gwamnatin Nasarawa ta baiwa Ilumi mahimmanci a kasafin kudi na 2024

Daga Zubairu Lawal

Cikin kasafin kudi na shekarar 2024 Gwamnatin jihar Nasarawa ta baiwa bangaren ilumi mahimmanci domin amfanar al’umman jihar.

Da take jawabi wajen bayyana guraben da za a kashe kudaden shekarar bana. Kwamishiniyar Kudi ta jihar Nasarawa Hajiya Munirat Abdullahi ta bayyana yadda aka shirya kashe kudaden shekarar domin gudanar da ayyukan raya kasa.

Tace; cikin kasafin Gwamnati ta ware zunzurutun naira biliyon 40.16 domin cimma muradin harkan ilumi a jihar..

Sannan naira biliyon 113.12 zai tafine wajen gudanar da manyan ayyukan cigaba jihar Nasarawa.

Manyan ayyukan sun hada da samar da hanyoyi a birane da jarkara da samar da tsaftacecen ruwansha  ga al’umman jihar Nasarawa da gina Asibitochi da magunguna.

Haka zalika cikin kasafin kudin akwai bangaren bun qasa harkokin matasa.Akwai batun tsaron lafiyan al’umman jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *