Ba da izinin Gwamna Sule Kotu ta tsare matan PDP 38 a Nasarawa ba – Piter Ahemba.

Ba da izinin Gwamna Sule Kotu ta tsare matan PDP 38 a Nasarawa ba – Piter Ahemba.
Daga Zubairu Lawal
Babu hanun Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule kan tsare masu zanga zanga da yamutsin bayan yanke hukuncin kotun koli a shari’ar zabe.
Mai taimakawa Gwamna a fannin yada labarai Kwamared Piter Ahemba ya bayyana haka a takardan da yarabawa manema labarai.
Kwamnared Piter Ahmba yace; jami’an tsaro suka kama masu ta da tarzoma kuma suka gurfanar dasu gaban kuliya.
Kwamared Piter Ahemba yace; masu kalubantar Gwamna masmman Shugabannin jam’iyyar PDP su sani mutani da suka tayar da tarzoma bayan hukuncin kotu ya zama dole jami’an tsaro su dauki matakin dakile yamutsin.
Kwamared Ahemba yace: bukatar zaman lafiya da hadin kan al’umma ake bukata a jihar Nasarawa.
Siyasa bazata rabakan al’umman jihar Nasarawa ba.
Maganganun Shugaban jam’iyyar PDP Mr Francis Orogu da magoya bayansu bai cancantaba. Bai kamata an jingina zantuka mara dadi ga Gwamna Sule ba.
Kwamared Piter Ahmba yayi kira ga al’umman jihar Nasarawa dasu rungumi zaman lafiya da cigaban jihar kamar yadda Gwamna Abdullahi Sule yake tafiyar da jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *