Kungiyar yan dako na taimakawa Gwamnati wajen baiwa matasa aiki a Nasarawa – Alhaji Danji Aliyu

Kungiyar yan dako na taimakawa Gwamnati wajen baiwa matasa aiki
Inji Alhaji Danji Aliyu

Daga Zubairu M.Lawal Lafia

Shugaban kungiyar yan dakon buhun hatsi ta jihar Nasarawa Alhaji Danji Muhammad Aliyu yayi kira ga Gwamnati jihar Nasarawa da ta waiwaye kungiyar yan Dako domin tana taimakawa Gwamnati wajen baiwa matasa ayyukanyi.

Shugaban Kungiyar yace: suna da mambobi matasa masu yawa.

Yace; Duk gurin da suka ga matasa suna zaman kashe wando babu aikinyi suna janyosu su koyar dasu sana’ar dako.

Yace: da haka zakaga mutum ya mike wasun gina gida wasun Aure wasu na karatu duk suna daukar nauyin karatunsu ko na yaransu cikin wanna. Sana’ar dako.

Yace: akaw wadanda sukayi karatu daga matakin Piramare zuwa Sakondire zuwa gaba da Sakondire duk a cikin wannan Sana’ar ta dako.

Shugaban kungiyar yan Dakon ya bayyana haka ne wajen bikin bude sabon ofishin kungiyar dake kasuwar hatsi na Kwandare dake garin Lafia.

Yace: cikin kudaden da kungiyar ke Tarawa suka gina wannan katafaren ofis.

Ya zuwa yanzu ofishin tana da motochin sufuri da wasu kaddarori mallakin Kansu.

Shima Shugaban kungiyar ta Qasa Alhaji Hamza Abdullahi ya yabawa jerin Shugabannin da suka jagiranci kungiyar tun farkon kafata har ya zuwa yanzu.

Yace: kungiyar tayi Shugabannin goma sha daya. Yace: a bays kungiyar tana samun Shigabannine ta hanyar nuna karfi. Duk lokacin da kan wasu ya hadu zasuzo da nuna karfi su kwaci mulki.

Yace; daga bays anbi tsarin zamani aka fara zaven Shugabannin.

Alhaji Hamza Abdullahi shima tsohon Shugaban ne da ya mulki kungiyar tsawon shekaru takwas.

Yace; tsarin da kungiyar tabi nayin zaven Shugabannin ya kawo cigaba so sai a kungiyar.

Abin birgewa ga kungiyar duk Shugaban da yayi komari to Wanda zai zo a bayanshi sai ya fishi.

Taron ya samu hakartan manyan baki da yan kasuwa da malamai, sannan an gudanar da adu’o’i domin samun zaman lafiya ga Nijariya da Jihar Nasarawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *