Adams Oshiomhole, ya daina tsoma baki a harkan Majalisa

Xan majalisar Dattawa mai wakiltar  mazaber Nasarawa ta Arewa Sanata Philip Gyunka ya bayyana haka a babban ofishin jami’iyyar PDP ta jihar Nasarawa a garin Lafia.
Yace; bazamutaba amincewa da dukkan yunkurin da Shugabannin Jami’iyyar APC keyi na ganin an sauya Shugaban Majalisar Abubakar Bukola Saraki daga kujerarsa ba.

yace ; ko kaxan bazasu amince da duk wata makarkashiya da ake shiryawa na tsige Saraki ba muddin ta sabawa doka .

Xan Majalisar ya kara da cewa ; Sanatocin PDP sun sanya idanu suna lura da duk wata yunkuri da za’ayi domin cimma wannan manufar.

Sanata Philip  Gyunka ya gargadi shugaban APC, Adams Oshiomhole, cewa batun tsige shugaban majalisa ta banbanta da gwagwarmayar kungiyoyi kwadago da ya saba yi a baya .saboda haka tsige Shugaban Majalisa ba karamin aiki bane yana bukatar cikakun sharuda ba kawai ingizu jama’a suyi bore bane.

Sanatan ya bayyana haka ne gaban dubban jama’a da suka tarbeshi wajen kaddamar da takardan tsayawansa takarar kujerar Gwamnan jihar Nasarawa a zaven Shekarar 2019 .

Xan majalisan Dattawan  ya ce ; ba zasu amince da duk wata makarkashiya da ake shiryawa na tsige Saraki ba muddin ta sabawa kundin tsarin mulki.

Sanata Gyunka, ya nuna damuwarsa kan yadda shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole, ke katsalandan cikin lamarin da tuni kundin tsarin mulkin Najeriya ta fayyace wanda ya kamata ya zama shugaban majalisar dattawa.

A cewarsa, kundin tsarin mulkin ta baiwa kowane dan majalisa ikon zama shugaban majalisa ba kamar mukamin Shugaban masu rinjaye da marasa rinjaye ba wanda dole su kasance daga jam’iyyar dake rinjaye ko akasin hakan.

Ya kuma ce akwai ka’idoji da doka ta shimfida kan yadda ‘yan majalisar zasu iya tsige duk shugaban da basu gamsu da irin kamun ludayinsa ba. “Doka ta fadi karara cewa duk lokacin da kashi biyu cikin uku na ‘yan majalisar suka nuna rashin gamsuwarsu da shugaba, toh babu makawa zasu iya tsige shi.

“Hakan yasa nake mamakin yadda Oshiomhole ke barazanar cewa dole sai an tsige Saraki duk da cewa shi ba dan majalisa bane.” cewar Sanata Gyunka. Yace Sanatocin PDP sun sanya idanu suna lura da duk wata fadin tashi da akeyi na  yunkuri abinda bazai haifar da damai mai ido ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *