Yunkurin tsige Saraki kan Sanatochin APC ya rabu biyu .

Rahotan da muka samu daga Daily Trust na nuna cewa an samau baraka tsakanin Sanatocin jam’iyyar APC a kan batun maye gurbin shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki.

Wasu daga cikin Sanatocin na ganin Sanata Ahmad Lawan (APC, Yobe) ne yafi dacewa ya maye gurbin

yayin da wasu kuma sun dage cewa Sanata Godswill Akpabio (Akwa Ibom) ne yafi cancanta da kujerar. Wata majiya ta ruwaito cewa shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole yace kan ‘yan jam’iyyar ya rabu gida biyu a taron kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka yi a ranar Talata. Kan Sanatocin APC ya rabu a kan magajin Saraki
taron da akayi a baya, an zabi Lawan a matsayin wanda zai maye gurbin Saraki da Sunny Ogbuoji (APC, Ebonyi) a matsayin mataimakinsa wanda zai maye gurbin mataimakin shugaban majalisa, Ike Ekweremadu.
A gudanar da taron na ranar Talata ne cikin sirri a Sheraton Hotel dake Abuja. Wani dan majalisa ya ce an kira taron ne saboda a duba yadda za’a warware rashin jituwar da ke tsakanin ‘yan majalisar tarayya da gwamnonin jiha amma an daga baya akallar taron ya karkata ga yadda za’a canja shugabanin majalisar Dattawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *