An Zantarmasa da Hukuncin kisa saboda ya Kashe Matarsa kan #1000

An yanke hukuncin kisa kan wanda ya kashe matarsa saboda #1000

Daga Zubairu  Lawal

Mai shari’a, Ntong Festus Ntong, na babbar kotun jihar Akwa Ibom dake zamanta a karamar hukumar Ikot Ekpene ta yanke hukunci a kan shari’ar wani magidanci da aka gurfanar bisa zarginsa da kisan matarsa mai dauke da juna biyu, shekaru hudu da suka gabata .

Kotun ta yankewa magidancin mai ‘ya’ya 7, Friday John Uko, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan gamsuwa da tuhumar da ake yi masa na zargin kisan matarsa Patience .

Alkali Ntong ya umarci a rataye Mista Uko, dan asalin karamar hukumar Ikot Ossom ta jihar Akwa Ibom, har sai ya mutu, a matsayin hukuncin laifin day a aikta tun watan Agusta na shekarar 2014.

Kotun ta yarda cewar Mista Uko ya bugi matarsa da kafa a ciki, yayin da take dauke da juna biyu a karo na takwas bayan aurensu, lamarin daya jawo mata ballewar jini da ya zama silar mutuwar ta.

Tun farko, dan sanda mai gabatar da kara ya shaidawa kotun cewar takaddama ta barke tsakanin Uko da marigayiya Patience bayan ta dauki kudi, N1,000, a aljihun rigarsa domin dafa abincin da zasu ci a gidan.
Da yake yanke hukunci a ranar juma’a, Alkali Ntong, ya bayyana fushinsa yadda Mista Uko ya kasha matarsa mai juna biyu, da ya kamata take lallabawa, aljuhunsa  kan N1,000. Alkali Ntong ya kara da cewa, “shari’ar ba wata mai sarkakiya ko daure kai ba ce tunda shi Mista Uko ya furta da bakinsa cewar shine ya jawo mutuwar matarsa saboda sabanin daya shiga tsakaninsu a kan N1,000.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *