Alumman Kano bazasu goyi bayan Kwankwaso ba

Alumman Kano bazasu goyi bayan Kwankwaso ba

– Ganduje

Daga Madina Ibrahim

Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa kanawa sun dade da kauracewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tuni sun wancakalar da tsohon Gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso.daga lamarinsu.

Ganduje ya ce idan har Kwankwaso ya isa ya shigo garin Kano ya kaddamar da kamfen din sa na neman Shugabancin Najeriya da yake shirin yi.

” Muna da damar mu wancakalar da shi, kuma mun riga mun yi watsi da shi tuni.

” Ba mu taba daukar sa Dan takarar Shugaban Qasa ba kuma ba za mu taba yin haka ba. Dan takarar Shugaban Qasarmu daya ne tak kuma shine Shugaba Muhammadu Buhari.

” Mu mutanen Kano zamu yi amfani da duk wata dama da muke da ita domin nuna masa iyakar sa, sannan mu tasa keyar sa mu nuna masa hanyar waje rod tun kafin zabe ma ta zo.

Ganduje ya amayo wadannan kalamai ne a wajen kaddamar da shirin baiwa mata 6,600 tallafin jari na 15,000 domin bunkasa sana’o’in su.

An yi rabon wannan tallafi ne a gidan gwamnati dake Kano ranar Lahadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *