Anyiwa Minista ruwan Duwatsu a Taraba

Anyiwa Minista ruwan Duwatsu a Taraba

Daga Zubairu Lawal

Ministan Harkokin Mata ta hadu da fushin wasu gungun Matasa daga Jihar dinta. Hajiya Jummai Al-Hasan ta hadu da fushin Matasanne a Qaramar hukumar Takum dake Jihar Taraba, a Lokacin da ta ziyarci Garin domin taimakawa Xan Jami’iyyarsu ta APC da ya tsaya a zaben cike gurbi na Majalisar Dokokin Jihar.

Dan takarar jam’iyyar PDP, Mista Garba Ajiya, ya lashe zaben maye gurbi na Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumat Takum a majalisar dokokin jihar Taraba da aka yi jiya, Asabar, 18 ga Agusta, 2018. Kamfanin dillancin Labarai na kasa (NAN) ta bayyana cewar an gudanar da zaben domin maye gurbin tsohon dan majalisa Hosea Ibi da masu garkuwa suka sace ranar 31 ga watan Disamba na shekarar 2017 kuma suka kasha shi a watan janairu na shekarar 2018.

Baturen Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Dakta Ayuba Kwada, ne ya sanar da sakamakon a daren jiya a karamar hukumar Takum.

Dakta Kwada ya bayyana cewar dan takarar PDP, Ajiya, ya samu Nasara a mazabu 5 daga cikin 6 da karamar hukumar ta Takum ke da su da adadin kuri’u 10,725, yayin da abokin takararsa na jam’iyyar APC, Mista Atem Ansho ya samu kuri’u 3,268 da samun nasara a mazaba daya kacal. Kazalika ya bayyana cewar an kada jimilllar kuri’u 14,717 a zaben amma 380 sun lalace tare da kin karbar sakamakon zabe daga mazabar Chanchanji saboda rashin biyayya ga dokokin zabe.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *