Babban rashi a Duniyar Fina-Finai ta Hausa
Daga Ibrahim
Allah ya yiwa Ayuba Dahiru Rasuwa Ayuba Dahiru yana daya daga Jarumi a masana’antar shirya finan-finan Hausa dake Kano, ya rasu da sanyi safiyar jiya Lahadi marigayin ya rasu a garin Kano bayan fama da gajeruwar rashin lafiya kamar yadda dareka a masana’antar Kannywood, Falalu Dorayi, ya shaidawa BBC Hausa.
“Allah ya yiwa Ayuba Tandu rasuwa bayan ya sha fama da zazzabi na kwana biyu. Muna masu addu’ar Allah ya gafarta masa,” in ji Falalu Dorayi. Marigayi Ayuba Tandu
Kafin rasuwar sa, Tandu ya fi fitowa a fina-finai ko matakin barkwanci. Wasu daga cikin fina-finan da ya fito sun hada da Auren Manga da Gobarar Titi da kuma Afrah. Ya rasu ya bar mata uku da kuma yara 9.