Baya Goya Marayu: Gwamna Tambuwal ya yiwa marayun Sakkwato sha tara na arziki

Baya Goya Marayu: Gwamna Tambuwal ya yiwa marayun Sakkwato sha tara na
arziki

Daga Madina Ibrahim

A shirye-shiryen shagulgulan Babban Sallah dake karatuwa, Gwamnan Jihar
Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya rabama wasu hakimai 86 zunzurutun
kudi N14.68 miliyan domin su siyawa marayu naman sallah a jihar.

Kamfanin dillancin labarai na Qasa NAN ta ruwaito cewa Gwamnatin Tambuwal
ta saba bayar da wannan tallafin duk shekara ta ofishin Zakka wanda aka
kafa a fadar Sarkin Musulmi Sultan Abubakar Sa’ad III.

A yayin da ake kafa kwamitin, Sultan Sa’ad Abubakar III ya jinjinawa
hakiman bisa irin jajircewa da goyon baya da suka bayar domin ganin shirin
yana samun Nasara a Garuruwansu.

Sarkin musulmi yace; Shirin ya yi Nasara sosai Saboda yana taimakawa marayu
wajen debe musu kewa da ganin cewa sunyi Shagalin Sallah cikin murna da
farin ciki kamar sauran jama’anm gari.

“Taimakawa marayu nauyi ne da ya ratayu a kan kowa da kowa Saboda hakan
akwai lada sosai daga wajen Ubangiji, ya kuma ce taimakon yana kawo cigaba
a Garuruwan “Saboda haka, ina kira ga dukkan wandanda aka daurawa nauyin
suji tsoron Allah wajen gudanar da ayyukansu Saboda su samu ladan gudanar
da ayyukan,” inji Sarkin Musulmi.

Sarkin musulmi ya mika godiyarsa ga Gwamnatin jihar Sakkwato da hukumar
Zaka na jihar Sakkwato saboda cigaba da gudanar da shirin. Ya yi addu’an
Allah ya taimakawa dukkan al’umman musulmi wajen gudanar da ibadunsu kuma
ya bukaci su rika yiwa Najeriya addu’an samun zaman lafiya da cigaba.

Tun da farko, Ciyaman din kwamitin Zakat, na Jihar,Alhaji Lawal Madoki, ya
ce shirin na cikin ayyukan Gwamnatin jihar ya ce wannan sha-tara-na arzikin
yana daya daga cikin yunkurin Gwamnati don taimakawa marayu da marasa
galihu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *