Likafa ta cigaba a duniyar Fina-Finan Hausa , Ali Nuhu ya samu Lambar Girmamawa

Likafa ta cigaba a duniyar Fina-Finan Hausa , Ali Nuhu ya samu Lambar
Girmamawa

Daga Zubairu Lawal

Wata Gidauniyar babbar Majami’ar mabiya addinin kirista ta nada daya daga
cikin Fitattun Jarumai a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood,
watau Alhaji Ali Nuhu a matsayin Jakadanta a kokarin ta na yaki da cin
hanci da rashawa.

Labarin da ya mamaye kafafen yada Labarai ta Yanar Gizo na cewa; Gidauniyar
cocin dai mai suna Big Church Foundation tsohon mijin fitacciyar jarumar
nan ta finafinan kudancin kasar nan Tonto Dikeh ne mai suna Olakunle
Churchill ya assasa ta domin rage shaye-shayen da ya addabi matasa a
Najeriya.

Jaridar Duniyarmu ayau ta samu cewa da yake gabatarwa da Ali Nuhu Shaidar
zaman sa Jakadar gidauniyar, Olakunle Churchill ya bayyana cewa tabbas ya
san yaki da shan kwaya ba karamin abu bane amma ya ce tabbas za suyi iya
bakin kokarin su wajen ragewanan mummunar dabi’a.

Jarumi Ali Nuhu dai fitacce ne a masana’antar shirya fina-finai a Najeriya
baki daya kama daga na Hausa har ya zuwa na turanci, wanda kuma Tauraronsa
ke Haskawa a Duniyar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *