Silas Agara ya cancanta ya zama Gwamnan Nasarawa
Inji Mrs.Aishatu
Daga Zubairu Lawal
Sunana Aishatu Isa Idoma jigoce a tawagar yakin niman zaven Xan takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a zaven 2019 Hon.Silas Ali Agara.
Ta bayyana cancantarsa da ya dace Jami’iyyar. APC ta tsayar da Hon. Silas Ali Agara a matsayin Xan takarar Gwamnan Jihar Nasarawa saboda kwarewarsa da sanin ya kamata da iya aiki .
Mrs. Aishatu ta bayyana Hon. Silas Ali Agara tace tankar Gwamna Umar Tanko Al-makura ne saboda karancin shekarunsa zaiyi amfani dasu wajen gyarar Jihar Nasarawa..
Ga yadda hirar ta kasance ayi sauraro Lafiya.
Dafarko zamuso muji sunanki?
Sunana Aishatu Isa Idoma
Na ganki cikin tawagar yakin niman zaven Xan takarar Gwamnan Jihar Nasarawa , kuma mukaddashin Gwamna Hon. Silas Ali Agara ko zakiyiwa masu karatu bayanin da ya sanya koke ganin ya dace jami’iyyar APC ta tsayar da Xan takarar Ku ?
Silas Ali Agara kowa yana yabonsa da halin kirki, a lokacin da na fara haduwa dashi munje ziyara a Jerusalem na ga halayensa na kwarai . daga baya mun hadu dashi cikin tawagar yakin niman zaven Gwamna Umar Tanko Al-makura ,naga iya aiki tare dashi kuma tsare-tsarenshi suna da kyau . yana daraja duk mutanin da suke gurin kuma yana karban shawara daga jama’a.
Yana girmama Sarakuna da kowa abokin maganarshine baya rena Magana ko abakinwaye yaji. Zaiyi bincike ko yabi diddigi idan maiyuwuwane ya aikata idan da shawara ya bada. Anan na kara sallamawa da irin yadda yake gudanar da aikinsa na tabbata kwararene .
Shiyasa da siyasa ya zo naga babu Wanda ya cancanata APC ta tsadashi takarar Gwamnan Jihar Nasarawa sai Silas Agara saboda yana da kwarewa da salon aikin cigaba kamar Babanmu Al-makura.
Kina ganin idan Agara ya zama Gwamna akawai alherin da mata zasu samu?
A vangaren siyasa mata sunaba da gudumawa kashi talatin da biyarne a Nasarawa . kuma wanan zaven na 2019 ina tabbatar maka wanda zaiyi maka zaka sani. Saboda Gwamnatin da muke ciki a yanzu ai baya bar mata a baya ba. Shima Silas Ali Agara badashi akeyiba? Ai ya gani kuma da shawarwarinsa cikin abubuwan da ake gudanarwa a wanan Gwamnatin.
Kaga kenan idan ya zama Gwamna a shekarar 2019 mata zasu mure fiye da yadda suke ci yanzu.
Ko akwai shawarar da zakiba Silas Agara saboda cigaban harkokin mata ,idan ya zama Gwamna?
Shawarar shine ya sanya mata cikin makaman da zai raba idan Allah yasa ya zama Gwamna. Mukamin Kwamishinoni ya sanya mata masu bada shawara ya sanya mata duk idan maza ke rike mukami a sanya mata ,idan akasa maza uku asa mata biyu .hakama mukaman Qananan hukumomi shima a sanya mata saboda mata susuke fita jefa kuri’a kuma mace zata iya janyo ra’ayin mace yar’uwanta saboda ciwon ya mace sai ya mace.
Sanan akwai hanyoyin da nasan Silas Agara zai bunkasa domin cigaban mata wadanda suke zaman gida. Akwai sana’o’in hannu wadanda za’abude a gurare da dama ana koyar da mata , idan sun iya a yayesu a basu jali suje suna gudanar da sana’ar domin dogaro da kai. Saboda ba kowata macece keda ilumin da zatayi aikin Gwamnati ba. Amma idan aka samar masu da hanyoyi harma da yan mata dama matasa ,idan yara sunje makaranta sun dawo zasuje gurin koyan sana’a kaga yara zasu tashi da sana’a ba sai sun dogara da aikin Gwamnati ba.
A jami’iyyar APC akwai yan takarar Gwamna da suka fito dayawa baki ganin zai haifar da rudani ?
A 2011 Babanmu Al-makura sun fito su uku a 2015 ansamu yan takarar da suka zarce hakan .kuma anyi zaven fidda gwani Babanmu Al-makura yayi nasara sauran sun amince da nasarar tashi sunhada kai aka tafi tare.saboda haka wanan karonmu ina rokon yan takara dasu hadakai idan anyi zaven fidda gwani wanda yayi nasara a bashi goyon baya a tafi tare.saboda matsayi na Allah ne
Wani kira kike dashi ga yan siyasa masamman na Jihar Nasarawa masu niman mukami ?
Mulki na Allah ne kuma yana ba wanda yakeso a lokacin da yaga dama. Kujerar Gwamna guda dayane nasan mutani sun fita dayawa suna bukata , ba’a hana kowaba saboda na mairabone. Wanda Allah yaga dama shi zai bashi. Bai kamata muyi siyasan ko a mutu ko ayi raiba. Saboda mulki zaka mulke jama’a ne idan babu jama’an wazaka mulka ?
Yakama ta yan takarar su sasanta kansu na kowata Jami’iyya ba sai APC ka dai ba dama PDP da APGA da sauran su . mu sani bamuda Jihar da ta wuce Jihar Nasarawa, bai kamata muyi sanadiyyar zubar da jini a Jihar Nasarawa ba. Ba saboda siyasa ba ko saboda menene.ya kamata muhadakai muga cigaban Jihar Nasarawa muyi aiki tare koda siyasa ba daya ba amma mu yan Jihar Nasarawa ne jiharmu daya.
Lokaci yayi da yansiya ya kamata adaina siyasan ko a mutu ko ayirai a siyasan Nijeriya saboda babu abinda yake haifarwa face cibaya.