Yankin Afirka nada bukatuwa a vangaren tattalin arziki
Inji Vera Songwe
Daga Zubairu Lawal
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya mai kula da vangaren tattalin arziki a nahiyar Afirka Mrs Vera Songwe tace; nahiyar tana bukatar hanyoyin bunkasar tattalin arziki
Vera Songwe ta bayyana hakan a wurin taron karawa juna sani da aka gudanar a kwanakin baya.
Manyan baki da suka samu halartan gurin taron sun hada da tsohon shugaban kasa Yakubu Gwawon, tsohon Ministan harkokin yau da kullun, sai tsohon mai wakiltar majalisar dinkin Duniya Farfesa Ibrahim Gambari.
Vera Songwe ta ce ; ya kamata Afurka su canja salon yadda suke amfani da arzikin da Allah ya basu, saboda hakan yana da matukar mahimmanci. Ta kara da cewa “dinbin arzikin da Afurka suke da shi na manfetir da sauran wasu abubuwa yaci ace suna sarrafashi a tsakaninsu ta yadda ko wata qasa zata ammafana da takwaroron su a Afurkan.
An dai shirya taron ne dan tunawa da Farfesa Adebayo Adedeji, wanda ya rike mukamin sakataren majalisar Dinkin Duniya mai kula da tattalin arziki a bengaren Afurka har na tsawon shekara 16. kuma an gudanar da taron ne a Blu otel dake Ikeja Logos a ranar Asabar din da ta gabata.
Taron dai an mai taken “cigaban tattalin arzikin Afurika darasin da zamu koya daga Adebayo.
Da yake jawabi a wurin taron, Tsohon Shugaban qasan Nijeriya Janaral Yakubu Gwawon yace; Adedeji kwararre ne a bangaren tattalin arziki a Duniya, ko yaushe burin shi ya ciyarda Najeriya gaba, bama Najeriya kawai ba har ma da Afurka gaba daya.
ya yi aiki tukuru a harkokin qasa da qasa na Dufulomasiya a tsakanin Afurka.
Qasashen Afurka dai da dama suka turo wakilan su a wurin taron.