Kasar Amurka ta zargi Gwamnatin Buhari da laifin kin daukar mataki
Daga Zubairu Lawal
Gwamnati Amurka ta zargi Shugaban Kansan Nijeriya Muhammad Buhari da rashin daukar matakai na nuna basani ba sabo gameda kasha-kashen da akeyi masamman a Arewacin Nijeriya
jaridar The Punch ta bayyana rahoton cewa, ‘kasar Amurka ta na zargin aukuwar kashe-kashe musamman a yankunan Arewa na Najeriya a sanadiyar rikon sakainar kashi da nuna halin ko oho.da Gwamnatin Nijeriya keyi game da rayukan alumman da ake kashewa.
Gwamnatin ‘kasar Amurka ta bayyana cewa, cigaba da aukuwar kashe-kashe a kasar nan ya bayu ne a sakamkon rashin daukan matakai gami da rashin tsauraran hukuci daga bangaren gwamnati.
Wani Manzo na Masamman a ofishin jakadacin kasar Amurka dake Najeriya, David Young, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai cikin birnin Jos dake jihar Filato a daren ranar Lahadin da ta gabata.
A yayin taron addinin Kirista da aka cikin wani coci a Jihar ta Filato, Mista Young yake cewa a sanadiyar halin ko in kula gamin da rashin daukan tsauraran Matamakai daga bangaren gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya ake cigaba da zubar da jini a kasar nan.
Ya kara da cewa: ya kamata gwamnatin Najeriya ta shimfida tsauraran matakai gami da dokoki na hukunta masu aiwatar da kashe-kashe a kasar nan. Mistte Young, ya kuma nemi gwamnatin Shugaba Buhari akan ta tabbatar hukumar zabe ta kasa wato INEC ta gudanar da gaskiya gami da adalci yayin gudanar da zaben 2019.
Kazalika, Dan aiken na kasar Amurka ya kuma kai ziyarar ban girma gami da jinjina ga Limamin nan mai shekaru 83 a duniya, Alhaji Abubakar Abdullahi, da ya yi ceton Kiristoci 300. yayin aukuwar wani harin Makiyaya a ranar 24 ga watan Yuli cikin kauyen Nghar dake gundumar Gashish a jihar ta Filato: