Kwankwaso yayi sallar idi a garin Shugaban APC yadda yaja zugar Jama’a
Daga zubairu lawal
Duk da kasancewar yaune ranar da aka gudanar da Bikin Babban Sallar Laya , akasarin yan Siyasa basuyi Sallah a garuruwansu ba suna can wasu guraren suna yawon niman zabe.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yayi sallar sa ne a Kudancin Najeriya garin Benin Babban Birnin Jihar Edo kuma Shugaban Jam’iyyar APC inda nan Sanatan ya gana da dubban magoya bayansa.yayin da yake cigaba da zagaye domin neman goyon bayan jama’a game da 2019.
Tsohon Gwamnan yayi sallah ne tare da Mabiya Kwankwasiyya da ke Yankin na Kudancin Najeriya. Kafin nan kuma Sanata Kwankwaso ya ziyarci fadar Oba na Benin Omo N’Oba N’Edo Uku’ Akpolokpolo Ewuare 11 domin tattauna wasu abubuwa da su ka shafi kasar nan.
Hadimin tsohon Gwamnan na Kano Hon. Saifullahi Hassan ya bayyana cewa Rabi’u Kwankwaso ya gana da Sarkin Nufawa Alhaji Umar Yabagi da kuma Sarkin Hausawa Alhaji Adamu Sheikh Abdulrazak na Jihar Edo
Haka zalika shima Gwamna Nasir El-Rufai ya garzaya Garin Kafanchan inda anan ne yayi bukin Babban sallar inda akayi masa Nadin Sarauta a matsayin Garkuwan Talakawa na Yankin Jema’a