Man city bata niman dan was an da zai maye gurbin Kebin De Bruyne daga wata Kungiya
-inji Guardiola
Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola, ya bayyana cewa baya neman tsohon dan wasan Jubentus, Claudio Marchisio wanda yabar kungiyar ta Jubentus a ranar Juma’a bayan ya shafe shekaru 25 yana bugawa kungiyar wasa. Marchisio, mai shekara 32 wanda ya buga wasanni 389 a kungiyar ta Jubentus ya lashe kofuna da dama a kungiyar sannan kuma ya buga wasanni da dama a kasar Italiya sai dai wasanni 20 kacal ya buga a kakar wasan data gabata.
A ranar Juma’a kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta bayyana cewa dan wasanta Kebin De Bruyne zaiyi jinyar watanni uku bayan daya samu rauni a lokacin da kungiyar take daukar horo a satin daya gabata.
Hakan yasa aka fara rade radin cewa shugabannin kungiyar za su fita neman wani dan wasa wanda zai maye gurbinsa kafin yadawo kuma tuni aka alakanta kungiyar da zawarcin Marchisio domin ya taimakawa kungiyar. “Tabbas munyi babban rashi na De Bruyne kuma zamuyi kokarin ganin rashinsa bai bamu matsala ba saboda yanzu aka fara gasa kuma akwai wasanni dayawa a gabanmu wadanda masu wahala ne sai dai muna fatan nan gaba zamu murmure” in ji Guardiola
Ya cigaba da cewa “Marchisio babban dan wasa ne wanda yayiwa Jubentus bauta kuma ya buga wasanni da dama a kasar Italiya saboda haka yana bukatar hutawa sosai amma dai yanzu munada ‘yan wasan da bama bukatar karin kowa” Manchester City dai itace ta lashe gasar firimiyar data gabata da maki 100 kuma a wannan kakar ta siyi dan wasa Riyad Mahrez daga kungiyar Leceister City akan kudi fam miliyan 54