Na cancanta nayi takarar Shugabancin Kasa

Na cancanta nayi takarar  Shugabancin Kasa

– Tambuwal

Madina Ibrahim

A ranar Litinin din da ta gabata ne

Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana cewa ya cancantane ya tsaya takarar Shugaban kasa , Gwamnan yace: da yaso yana da duk wata buƙata da cancanta ta ƙalubantar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jam’iyya mai ci ta APC.

Gwamnan  ya furta wannan kalaman gami da bugun kirji tare cika murza gashin baki, cewa, da ya so tun a lokacin zaben fidda Gwani a Shekarar 2015 da yafito

Ya tabbata yana da duk wata cancanta ta yin fito na fito wajen takarar fitar da gwani tsakanin sa da shugaba Buhari a karkashin jam’iyyar APC.

Cikin Kalamansa yayin da yake maida martini ga Tsohon Gwamnan jihar Lagos Asiwaju Ahmad Bola Tunubu, da yake cewa Gwamnan ya fice daga Jami’iyyar APC ne saboda tunanin ba za’a bashi Tiket na tsayawa takaran ba.

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya bayyana cewa, Tambuwal ya sauya sheka ne zuwa jam’iyyar adawa ta PDP sakamakon fargaba ta rashin samun tikitin jam’iyyar wajen ƙalubalantar Shugaba Buhari yayin zaben fitar da gwani. 2019:Dan haka Tambuwal ya kara da cewa: Ina da duk wata cancanta ta ƙalubalantar Shugaba Buhari

Gwamnan ya maida wannan martaninne cikin shafin sada zumunta ta fadar Gwamnatinsa ranar Littinin da ta gabata.

 

 

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *