Saraki ya yiwa Tunubu har tonon silili
Daga Madina Ibrahim
Shugaban majalisar dattawa ta Kasa Abubakar Bukola Saraki, ya maitawa Tunubu martini cikin bacin rai.
Saraki yace; dalilin da ya sanya kanwa uwar gamin matsalolin jam’iyyar APC watau Asiwaju Bola Tinubu, ke ci gaba da goyon bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari. Ido rufe saboda yana nada masa tarkon nan gaba.
Saraki ya bayyana cewa, Tinubu na ci gaba da goyon bayan zarcewar shugaba Buhari a karo na biyu yayin zaben 2019 domin ya ci gajiyar kujerar a shekarar 2023.
Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, Saraki ya bayyana wannan Martanin cikin wata sanarwa a ranar Litinin din da ta gabata dangane da rubutun kan wata budaddiyar wasika da Tinubu ya rubuta a ranar Lahadin da ta gabata.
cikin budaddiyar wasikar sa ya bayyana cewa, Shugaban majalisar dattawan ya yi watsi da jam’iyyar APC ne kadai domin cimma manufar sa ta neman kujerar Shugaban kasa da ba ta da wani tushe face na son zuciya.
Saraki yace; Tunubu shine aba’isar dukkanin matsalolin da suka addabi Jami’iyyar APC., sakamakon karfin da aka mika masa na jan ragamar Jam’iyyar.ya kara da cewa; Tinubu ya zama kanwa uwar gami wajen hadasa dukkanin rigingimu domin ganin ya cimma muradunsa a 2023.
Ya kara da cewa Tunubu,kadan ba ya alfahari gami da rashin gamsuwa dangane da yanayi na jagorancin shugaba Buhari, amma haka zai cigaba da jajircewa wajen goyon bayan sa domin samun dama ta cin gajiyar kujerar sa a shekarar 2023 kamar yadda Saraki ya bayyana.