matasa sun cinna wa kotun majistare wuta a Orlu
daga Ibrahim Mustapha
wasu gungun Matasa a garin Orlu ta jihar Imo sun bankawa wato kotun majistare wuta.wuta tayi barna inda wasu mahimman takardu suka kone kafin a iya shawo kan wutan ta kona abubuwa da dama a cikin Kotun.
Kotun majistare din na a cikin harabar babban kotun Orlu ne. sai dai Kakakin yan sandan jihar, Enwerem wadda ya tabbatar da lamarin ga manema labarai ya bayyana cewa an sanya wannan wuta da gangane ba bias kuskure ba. Ya kara da cewa; Rundunar Yan sanda ta tashi haikan wajen ganin ta zakulo wadanda suka aikata wannan laifin a hukuntasu.