Takarar Gwarzon dan wasan Nahiyar Turai Modric Da Ronaldo Da Salah Suna kan gaba.

Takarar Gwarzon dan wasan Nahiyar Turai Modric Da Ronaldo Da Salah Suna kan gaba.

Daga Madina Ibrahim

An bayyana sunayen Gwarazan da tauraronsu ke haskawa a bangaren was an Kwallon kafa ta a Nahiyar Turai ‘yan wasa Luka Modric da Cristiano Ronaldo da Mohamed Salah cikin jerin farko na ‘yan wasan da ke takarar gwarzon dan wasan zakarun Turai, UEFA, na bana.

Kwamitin da ya kunshi alkalan wasa 80 da ‘yan jarida 55 ne ya zabi dan wasan tsakiya na Real Madrid wato Luka Modric, dan wasan gaba na Jubentus Ronaldo da kuma dan wasan gaba na Liberpool Muhammad Salah domin yin takarar.

Za a ba da kyautar gwarzon dan kwallon kafar ne lokacin da za a yi wasannin rukuni na gasar cin kofin zakarun Turai a Monaco ranar 30 ga watan Agusta. An bayyana sunayen Pernille Harder, Ada Hegerberg da kuma Amandine Henry domin fafatawa don zama gwarzuwar ‘yan kwallon kafar UEFA ta mata a bana.

‘Yar wasan gaba ta Denmark Harder tana buga wa Wolfsburg wasa, yayin da ‘yar wasan gaba ta Norway Hegerberg da ‘yar wasan baya ta Faransa Henry ke buga wasa a Lyon.

Cikin Jerin wadanda ke takarar a bangaren Maza  Ronaldo,shine kadai ya taba lashe wannan kautar ta Zakarar Kwallon kafa,  wanda a yanzu haka ya koma Jubentus daga Real Madrid a watan Yuli a kan £99.2m, ya taba lashe gasar a 2017,shine kambun ke hannunsa har yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *