Yan Bindiga sun kai farmaki  gidan sanata Akpabio

Yan Bindiga sun kai farmaki  gidan sanata Akpabio

 

Daga Ibrahim Mustapha

Wasu mahara da baa tantance ko suwayeba sunkai farmaki gidan tsohon Shugaban marasa rinjaye a Majalisar dattawa ta Kasa Sanata Godwill Akpabio

Rahotanni sun kawo cewa wasu yan bindiga sun kai mamaya mahaifar sanata Godwill Akpabio a ranar Talata, 21 ga watan Agusta da misalin karfe 7:30 na yamma a jihar Akwa Ibom, inda yake gabatar da taron siyasa jaridar Premium Times ta ruwaito.

Hadimin mista Akpabio a shafukan zumunta, Anietie Ekong ya bayyana hakan a shafin Facebook a daren ranar Talata. Mista Ekong ya rubuta a shafin zumunta, “yanzu haka: wasu yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba na harbi a Ukana Ikot Ntuen, karamar hukumar Essien Udim, mahaifar tsohon Shugaban Marasa rinjaye a Majalisar Dattawa, kuma tsohon Dan Jam;iyyar PDP Sanata Godswill Akpabio.

“Jami’an yan sandan yankin Essien Udim da kwamishinan yan sandan jihar Akwa Ibom sunyi gaggawan kawo doki.zuwa wajen da abin ke faruwa” Okupe Wasu daga cikin mutanen dake zama kusa da gidan Akpabio a Ukana Ikot Ntuen, Essien Udim, sun bayyana cewa sun lura da motocin yan sanda da yawa da aka ajiye a gaban gidan sanatan da safe, misalin karfe 6:30. Hadimin nasa yace Sanatan na cikin koshin lafiya I zuwa  safiyar yau

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *