Buhari ya kakkabawa Nijeriya bashi a shekara 3
– Ben Murray Bruce
Aliyu Mustapha
Sanatan Yankin Bayelsa ta Gabas Ben Murray Bruce ya bayyana cewa Gwamnatin APC ta Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta karbowa Najeriya makukun bashi bayan hawan ta mulki shekaru 3 da su ka wuce. Sanata Ben Murray Bruce ya kalubalanci cin bashin da Gwamnatin APC tayi.
Sanata Ben Murray Bruce yayi kaca-kaca da Gwamnatin Buhari game da halin tattalin arzikin da Najeriya ta ke ciki. ‘Dan Majalisar yace Gwamnatin Buhari ta ci bashin da ya haura abin da PDP ta ci tun daga shekarar 1999.
Ben Bruce yace babu wani cigaban tattalin arzikin da aka samu a Gwamnatin Buhari. Sanatan ya nemi Jam’iyyar APC mai mulki tayi wa mutanen kasar nan bayanin inda aka kashe bashin da aka ciyowa Najeriya daga 2015 zuwa yau. Yace abin dubawani saboda babu wani aikin azo again da Gwamnatin tayi amma taciyo bashi da zai gagari kasan nan biya nana kusa.