Dan Arewa zaiyi takarar Shugabancin Kasa a Jam’iyyar APGA

Dan Arewa zaiyi takarar Shugabancin Kasa a Jam’iyyar APGA

Daga Madina Ibrahim

Jam’iyyar APGA ta bayyana yankin Arewa a matsayin yankin da Dan takararta na Shugabancin Kasa zaifito a zaben 2019 kwamitin amintattu na jam’iyyar APGA ta bayyana cewar dan takarar su na Shugaban kasa zai fito daga arewacin Najeriya . Bayan tashi daga wani taro na Shugabannin jam’iyyar day a gudana a Awka, babban birnin jihar Anambra. Jam’iyyar APGA ta bayyana cewar ta mika kujerar takarar shugaban kasa ga yankin Arewa sannan dan takarar Mataimakin Shugaban kasa zai fito daga yankin kudu maso gabas..

A takardar sanarwa da jam’iyyar ta fitar, ta sanar da cewar ta gudanar da taron ne a fadar gwamnatin Anambra a matsayin karramawa ga jagoran APGA na kasa, Gwamna Willie Obiano. Dan takarar Jam’iyyar APGA a zaben 2015, Dan takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a karkashin Jam’iyyar APGA Hon.Labaran Maku  ya bayyana cewar jam’iyyar APGA ta tattauna muhimman batu da suka shafi makomar ta da kuma lamuran da suka shafi siyasar Najeriya.

Musamman zaben shekarar 2019 mai zuwa. Da yake karin bayani ga manema labarai a garin na Awka, Sakataren kwamitin amintattu na APGA, Alhaji Sani Shinkafi, ya bayyana cewar jam’iyyar zata samar da dan takara daga Arewa da zai warware matsalolin Najeriya idan ya ci zabe. Da yake amsa tambaya a kan mutumin da jam’iyyar zata tsayar takara, Shinkafi, ya ce tabbas akwai babban dan siyasa daga Arewa da APGA zata tsayar. Sai dai bai ambaci suna ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *