“Sai na biya matata kudi sannan nike kwanciya da ita”

“Sai na biya matata kudi sannan nike kwanciya da ita”

Daga Zubairu Lawal

Wata mata na karbar kudi kafin mijin ta ya kwanta da ita – Lamarin na faruwa ne a jihar Oyo – Mijin ne ya fadawa alkali haka Wani magidanci mai shekaru 35 a duniya mai suna Mista Yinka Alabi a ranar Juma’ar da ta gabata ya kai karar matar sa wurin alkalin kotun majistare dake a unguwar Agodi, garin Ibadan babban birnin jihar Oyo.

“Sai na biya matata kudi sannan nike kwanciya da ita” Karar dai wadda ta dauki hankalin al’umma da dama, tana da dangantaka ne da yadda yace matar sa mai suna Funmilola na karbar masa kudi a duk lokacin da zai kwanta da ita. Duniyarmu ayau ta dauko daga shafin NAIJ.com ta samu cewa sai dai mijin ya bukaci alkalin kotun da ya ja mata kunne kawai domin kuwa yana son ta duk da bukatar saki da matar ta gabatar a gaban alkalin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *