Shin ko Kwankwaso zai kaddamar da tsayawa takarar Shugaban kasa a Kano ?
Daga Madina Ibrahim
Tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sa ranar kaddamar da takarar Shugaban kasa a zaben 2019 a karkashin Jam’iyyar PDP.Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai kaddamar da shirin sa na tsayawa takarar Shugabancin Kasa cikin wanan makon.
Kwankwaso na sa ran samun tikitin a Jam’iyyarsa ta PDP a zaben fitar da gwani da za ayi. A ranar Laraba 29 ga Watan Agustan nan ne Sanatan Kano ta tsakiya zai shirya taron tabbatar da tsayawa takarar Shugaban kasa a zaben da za ayi shekara mai zuwa. Za ayi wannan gangamin ne a babban Birnin Tarayyar Abuja sabanin jihar Kano kamar yadda wasu ke bayyanawa.
Kamar yadda mu ka samu labari, za ayi taron ne a filin taro na Eagles Square da misalign karfe 10:00 na safe. Ana tunani jama’a da dama musamman Magoya bayan babban ‘Dan siyasar za su cika Garin Abuja domin wannan taro na musamman.
Kawo yanzu dai tsohon Gwamnan yana cigaba da ganawa da manyan PDP na Kasar daga ciki har da tsofaffin Shugaban kasa irin su Goodluck Jonathan. A makon jiya kuma Kwankwaso ya gana wani jigo a PDP Tsohon Gwamna James Ibori. Dazu kun ji labari cewa Rabiu Kwankwaso ya kai wa Gwamnan Taraba Darius Ishaku ziyara a Abuja yayin da yake cigaba da shirin neman tsayawa takara a zaben na 2019. Shugaban na ‘Darikar Kwankwasiyya zai nemi doke Buhari a 2019