Ba Ni Da Matsala Da Shugabannina, Man United

Ba Ni Da Matsala Da Shugabannina,

Inji Mourinho

Daga Aliyu Mustapha

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ya bayyana cewa bashi da matsala da shugabannin kungiyar ta  duk da rade radin da ‘yan jaridu sukeyi na cewa basa ga miciji da juna. Rahotanni dai sun bayyana cewa Mourinho da shugaban gudanarwar kungiyar Ed Woodward basa ga miciji sakamakon rashin siyo masa ‘yan wasan daya bukata sannan shima kuma shugaban gudanarwar baiji dadin yadda aka doke kungiyar ba a satin daya gabata. Sai dai Mourinho ya bayyana cewa shi baya tattauna irin wannan maganar hasali ma bai san daga inda take fitowa ba kuma suna zaune lafiya da shugabannin kungiyar babu wata matsala da mutane suke fada. “Ba ni da matsala da shugabanni na kuma bani ne yakamata a tambaya ba saboda bansan komai ba saboda bana jin labarai bana karanta jaridu sannan bana kallon labarai a Talabijin kawai aikina nakeyi” in ji Mourinho Tun kafin a fara kakar wasa dai Mourinho yayi zargin shugaban kungiyar baya goyon bayansa ta hanyar siyo masa sababbin ‘yan wasa halin dayasa Mourinho yayi hasashen cewa idan basuyi wasa ba zasusha wahala a wannan kakar. Manchester United dai tasha kashi a hannun kungiyar Brighton Albion a ranar Lahadin data gabata kuma a gobe Litinin zata karbi bakuncin kungiyar kwallon kafa ta Tottenham a filin wasa na Old Trafford

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *