Duniya bazata manata da rawar da Kofi Annan ya taka ba

Duniya bazata manata da rawar da Kofi Annan ya taka ba

Sakataren MDD

Daga  Zubairu Lawal

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya mustab Antonio Guterres ya bayyana haka lokacin da yake Jawabi game da Mutuwar Kofi Annan .

Yace;  Marigayi Kofi Annan abun koyi ne ga sauran Mutane.Lokacin da aka sanar dani mutuwarsa  na kidime sosai da jin mutuwar sa.

Duniya bazata manta dashiba Ta hanyoyi da yawa saboda Kofi Annan wani vangare ne na Masalisar Dinkin Duniya. Ya rirrike muqamai da daman gaske a kungiyoyi daban-daban da kuma sauren vangarori na aiki. Kofi Annan ya koyar da duniya dabarun yadda za’a zauna Lafiya da juna tsakanin mabambamtar qasa da mabambamtar yare. Dama mabambamtar addinai.

hakan yasa ya taka babban matsayi a cikin al’umma kuma ya zama abun ko yi ga rayuwar alumma.

“Kamar yadda na ke cewa ina alfahari da Kofi Annan a matsayin aboki na kwarai abun koyi na kuma. kullun ina alfahari da matsayin da ya kaini na babban Kwamishina a bangaren ‘yan gudun Hijira a lokacin da yake babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya.
Dan haka zan kasan ce a rayuwata wanda zan dinga tunawa da shi, kuma zan dinga bin hikimomin irin mulikin da yayi a Majalisar Dinkin Duniya”. Shi dama al’adan shi ne duk inda yaje sai ya daura mutanin da ya tarar a wajen akan turba, kuma duk ma’aikatar da ya shiga sai ya warware musu duk matsalolinsu dake daminsu.

Ko da ya yi ritaya a Majalisar Dinkin Duniya, to, bai dakatar da aikin da yake ma majasalisar ba. Kuma har yanzu ana amfani da wasu abuwa wanda ya shimfida a Majalisar.

Dan haka ina mika sakon gaisuwa na a cikin jimami ga  Kofi Anann, da gaba dayan dangin shi, da kuma daukacin Mutanen Afirka, dama na Duniya gaba daya na wannan shahararren gwarzo wanda ya tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a gaba dayan Duniya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *