Kungiyar Arsenal Za Ta Kori Kociyanta nan gaba kadan – Adams
Daga Aliyu Mustapha
Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal,Tony Adams ya bayyana cewa sabon kociyan kungiyar bazai dade ba yana aiki da kungiyar idan har yaci gaba da buga salon wasan da kungiyar take bugawa a yanzu. Sabon kociyan kungiyar, Unai Emery, wanda ya maye gurbin Wenger a yafara buga wasanni biyu na firimiya da rashin nasara bayan yayi rashin nasa a hannun Manchester City da Chelsea a sati biyun da suka gabata. Sai dai duk da haka Tony Adam yana ganin halin da kungiyar take ciki a yanzu ba irin salon wasan da suke bugawa yakamata su dinga bugawa ba saboda an samu canjin mai koyarwa hakan yana nufin komai sai ya canja. “Na kalli wasan Manchester City da Arsenal kuma irin yadda kungiyar take buga wasa a lokacin Wenger haka aka buga babu wani canji amma kuma idan hakane baza a samu nasara ba saboda ana bukatar canji” in ji Tony Adams Ya ci gaba da cewa “ Akwai manyan kungiyoyin da suke buga irin salon wasan da Arsenal take bugawa amma kuma banbancinsu da Arsenal shine sunfi Arsenal kudi sannan suna da manyan ‘yan wasa ba kamar Arsenal ba” A karshe yace shugabannin kungiyar ne kawai suke boye boye basason su fitar da kudi su siyi ‘yan wasa sannan kuma su dauki mai koyarwar da zaiyi musu bore kamar Wenger, ma’ana wanda bazasu juya ba
