Gwamnatin Buhari ta gina wa ‘yan kudu tituna da gadoji 69
Zubairu Lawal
A ranar Litinin, 27 ga watan Agusta, gwamnatin tarayya ta fitar da jerin ayyukan ginin tituna da gadoji da ta ce tana yi a kudu maso gabashin Najeriya.
Ministan yada Labarai da Al’addu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewa ayyukan sun hada da tituna da gadoji 69 a yankin. A wata sanarwa daga hannun kakakin ministan, Segun Adeyeni yace ko da yake an bayar da wasu daga cikin kwangilolin gina hanyoyi da gadodjin kafin hawan wannan gwamnati kan mulki,amma ba a ba da kudi da yawa ko ma a wani lokacin ba a bayar da su ba kwata-kwata, domin gudanar da ayyukan.
Ministan yada Labarai Alhaji Lai Muhammad ya ce ayyukan da ake yi sun shafi dukkan jihohi biyar na yankin kuma suna matakai daban-daban na kammaluwa.
Ya kara da cewa an samu kudin yin ayyukan ne daga kasafin kudin da gwamnati ta yi da kudin da aka samu daga takardun lamuni na Sukuk da kuma asusun shirin Shugaban kasa na aiwatar da manya ayyuka. Daga karshe ya ce gwamnati na duba yiwuwar amfani da kudin da aka kwato daga barayin kudin Gwamnati domin aiwatar da ayyyukan ci gaban kasa a duk fadin Najeriya.