Gwamnatin Buhari ta gina wa ‘yan kudu tituna da gadoji 69

Gwamnatin Buhari ta gina wa ‘yan kudu tituna da gadoji 69

Zubairu Lawal

A ranar Litinin, 27 ga watan Agusta, gwamnatin tarayya ta fitar da jerin ayyukan ginin tituna da gadoji da ta ce tana yi a kudu maso gabashin Najeriya.

Ministan yada Labarai da Al’addu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewa ayyukan sun hada da tituna da gadoji 69 a yankin. A wata sanarwa daga hannun kakakin ministan, Segun Adeyeni yace ko da yake an bayar da wasu daga cikin kwangilolin gina hanyoyi da gadodjin kafin hawan wannan gwamnati kan mulki,amma ba a ba da kudi da yawa ko ma a wani lokacin ba a bayar da su ba kwata-kwata, domin gudanar da ayyukan.

Ministan yada Labarai Alhaji Lai Muhammad  ya ce ayyukan da ake yi sun shafi dukkan jihohi biyar na yankin kuma suna matakai daban-daban na kammaluwa.

Ya kara da cewa an samu kudin yin ayyukan ne daga kasafin kudin da gwamnati ta yi da kudin da aka samu daga takardun lamuni na Sukuk da kuma asusun shirin Shugaban kasa na aiwatar da manya ayyuka. Daga karshe ya ce gwamnati na duba yiwuwar amfani da kudin da aka kwato daga barayin kudin Gwamnati domin aiwatar da ayyyukan ci gaban kasa a duk fadin Najeriya.

Daga Zubairu Lawal

 

 

Leah Sharibu ta yi magana karo na farko a hannun Boko Haram

Daluba a makaratan Dapchi daya tilo data rage hannun Boko Haram tayi magana – Ta bukaci Gwamnati ta ceci rayuwarta Leah Sharibu, Daya daga cikin yan matan Dapchi 119 da yan Boko Haram suka sace a makarantan Sakandaren Gwamnati na mata a garin Dapchi, jihar Yobe, ta bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya ceceta. Leah Sharibu ce kadai ba’a saki ba lokacin da aka saki sauran yan matan saboda ta ki sauya addininta zuwa Musulunci.

A wani hoto da odiyo na nuna cewa tana da rai. Jaridar The Cable ta samu rahoto na musamman da ya kunshi hotonta da gajeren jawabi.

A jawabin, ta bukaci Buhari ya cetota kuma a taimakawa iyayenta da sauran iyalai. Sauran yan matan Dapchin da akayi garkuwa da su sun samu yanci sabanin mutane biyar da suka rasa rayukansu da kuma Leah Sharibu.

Boko Haram ta yi ikirarin kai harin sace yan matan kuma sun ki sakin Leah Sharibu na tsawon watanni bakwai yanzu. Gwamnatin tarayya ta ce tana iyakan kokarinta dan ceto Leah.

A hoton da jaridar The Cable ta samu, an ga Leah sanye da Hijabi kuma ta yi magana cikin sanyi. Wannan faifan odiyo da hoton da ya bayyana ya nuna cewa ana tattaunawa tsakanin gwamnati da yan Boko Haram kan sakin Leah Sharibu

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *