Za’a harantawa Kwankwaso Kaddamar da Takarar Shugabancin kasa  a Abuja

Za’a harantawa Kwankwaso Kaddamar da Takarar Shugabancin kasa  a Abuja

Daga Madina Ibrahim

A gobe Larabane ake saran Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai kaddamar da takarar niman  Shugabancin Kasa a birnin tarayya Abuja maimakon Jihar kano, Kwatsam sai ga wata Labarin da bayyiwa dubban masoyansa dadiba duk da cewa sun cika birnin Abujan.

Gwamnati ta hana Kwankwaso dandalin daya shirya kaddamar da takararsa a ciki

Kaddamar da yakin neman zaben Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na burinsa na tsaya takarar Shugaban kasa ya gamu da babban cikas a lokacin da Gwamnatin tarayya ta hana shi amfani da dandalin Eagle da kuma tsohuwar filin fareti na Sojoji, duk a babban birnin tarayya Abuja.

A ranar Litinin, 27 ga watan Agusta ne kwamitin yakin neman zaben Kwankwaso ta sanar da Kwankwason zai kaddamar da yakin neman zabensa a ranar Laraba 28 a babban birnin tarayya Abuja.

Sai dai jaridar Daily Nigerian ta an kammala duk wasu shirye shiryen fara taron kenan sai manajan dandalin Usman Raji ya hana kowa shiga dandalin, inda ya aika da wata wasika dake cewa Gwamnati ta hana Kwanwkaso amfani da dandalin ne don kada a takura ma ma’aikata dake sakatariyar ma’aikatan gwamnatin tarayya.

“Ku yi hakuri ba zaku samu damar gudanar da taronku a ranar da kuka tsayar ba, saboda taro ne na siyasa, kuma ranar 29 ga watan Agusta ranar aiki ne, don haka taron zai takura ma ayyukan ma’aikatan dake sakatariyar Gwamnatin tarayya.

Ku yi mana afuwa.” Inji wasikar. Haka zalika majiyarmu ta ruwaito wasu mjiyoyi dake nuna cewa hukumar tsaro ta farin kaya ta baiwa Kwankwaso umarnin yin taronsa, amma hukumar Yansanda ta ki bashi hadin kai, ya kara da cewa an hana su amfani da duk wani wajen Gwamnati, yanzu ya rage su kama hayar dakunan taro.

Sai dai duk da wannan tsaikon da aka samu, magoya bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na cigaba da tururuwa zuwa babban birnin tarayy Abuja don halartar gangamin, sai dai babu wani tabbaci game ko taron zai gudana a gobe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *