2019 Silas Agara ne Xan Takararn Gwamna a Nasarawa
Inji NLC
Daga Zubairu T M Lawal Lafia
Tawagar kungiyar Kwadago karkashin jagorancin Shugabanta na Jihar Kwamared Abdullahi Adeka sun bayyana goyon bayansu ga Xan Takarar Gwamnan Jihar Hon.Silas Ali Agara a 2019
A ranar Talata da tagabatane tawagar Kungiyar Kwadago ta Jihar Nasarawa tare da wasu gungun Jama’a suka kai ziyara ta masamman ofishin Mataimakin Gwamnan jihar Nasarawa Hon. Silas Ali Agara.
Da yake jawabi Shugaban Kungiyar Kwadagon yace; Daukacin ilahirin Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Nasarawa gaba daya sun amince da Mataimakin Gwamnan a matsayin Wanda zai gaji Gwamna Umar Tanko Al-makura a shekarar 2019 .
Yace; kungiyar ta amincene saboda ganin cancantarsa da kuma kwarewarsa a matsayin Wanda aka dade ana damawa dashi cikin harkan Gwamnatin Jihar. Sanan yasan damuwar Ma’aikata Kuma zai sharewa Ma’aikata hawaye .
Ya kara da cewa; yunwan Ma’aikata a jihar nan shine a tsayar masu da xan takarar da yasan mahimmanci aikin Gwamnati, shine wanda zai kyautatawa ma’aikata. Yace; tunda akeyin Mataimakin Gwamna a Jihar nan ba atabayin Mataimakin Gwamna kamar Silas Ali Agara ba saboda bashi da damuwa baya rikici da kowa kuma yanabaiwa Gwamnan shawara mai’amfani.
Ya kara da cewa; abubuwan cigaba da Agara yarika baiwa mai gidanshi shawara ,ciki harda kyautatawa Ma’aikatan Gwamnati. Saboda haka yanzu gamayyara Ma’aikatan Gwamnati sun amince da takarar Mataimakin Gwamnan a matsayin Wanda zai haye kujerar Gwamnan Jihar Nasarawa a 2019.
“Inada tabbacin idan Silas Ali Agara ya zama Gwamna a jihar Nasarawa damuwar Ma’aikata da yan kasuwa ya kare. Saboda Silas Agara mutum ne mai sauraron koken Jama’a. Sanan za’a samu yalwar tattalin arziki da cigaban qasa.”
Yace; Marasa aikinyi za’a samar masu da aiki da suma zasu dogara da kansu . za’a kuma fadad hanyoyin shiga da fice na kudaden shiga a Jihar.
Kungiyar Kwadagon tayi kira ga alumman Jihar Nasarawa dasu hada kai domin zaven xan takara na gari wanda zai kawo abin alheri a jihar da cigaban alumman Jihar da zaman Lafiya.
Sanan tayi kira ga dukkanin Ma’aikatan Gwamnati dasu gaggauta zuwa yanka katin zave saboda da shine zaka zave xan takarar da zai kwato maka yanci.
.kididdigar alkaluman alumman Jihar Nasarawa yana nuna jama’a da dama suna nuna kaunarsu ga takarar Mataimakin Gwamna Hon. Silas Ali Agara saboda ya kasance shine Wanda bashi da hayaniya cikin sauran yan Takarar.
Kuma shine xan takara daya tilo da ko dayaushe ofishinshi a bude yake kodaga ina mutum ya taho yana sauraronsa. Duk da cewa yana matsayin Mataimakin Gwamna amma alumma na shiga ofishinsa kamar kasuwa.
Yan Takarar Gwamna a karkashin Jami’iyyar APC sun kai kimanin 21 amma duk cikansu sun tattara sun tare a Birnin Tarayya sun mance da cewa a Jihar Nasarawa ne zasuyi mulki . kuma alumman Jihar ne suke bukatar abu agaresu.
Wanan ya sanya alumman Jihar basu ganin akasarin yan takarar da kimar cewa kosun zama Gwamna zasuyi masu abin azo agani.
Shi kuwa Mataimakin Gwamna kuma Xan takarar Gwamna Hon. Silas Ali Agara barin kofar ofishinsa dana gidansa a bude kowa ya shiga ya janyo masa karin farin jini wajen jama’a.
Saboda yanzu shine yafi kusa da jama’a sabanin wadanda ke zaune a Abuja. Kuma shike ganin jama’a a koda yaushe ofishinsa cike yake da Jama’a.
Sakamakon yadda Gwamnan Jihar Alhaji Umar Tanko Al-makura yake mika masa ragamar Jihar idan bayanan.
Hakan ya kara masa farin jini da