An kama wata mahaukaciya mai sayar da sassan jikin Mutum a Legas

An kama wata mahaukaciya mai sayar da sassan jikin Mutum a Legas

Daga Madina Ibrahim

Rundunar yan sanda ta tabbatar da kama wannan matar mai haukan karya, inda tfakewa da Hauka ta kasha mutani tana sayara da sassan jikinsu ga mabukata.

Duniyarmu ayau ta samu Labari yadda Asirin wannan baiwar Allah yacika Rundunar Yansanda suka cika hannunsu da ita, inda ayanzu haka take hannun hukumar ana tatsan bayanai daga gareta.

an yi ram da wata mahaukaciyar karya dauke da gawan mutum da ma wasu bangarori na jikin ‘Dan Adam a karkashin wata gada a Yankin Ojo da ke cikin tsakiyar Garin Legas.

Rundunar ‘Yan Sandan ta tabbatarwa manima Labarai da gaskiyar wannan al’amari. cewa asirin wata mahaukaciyar karya mai suna Folake Folade ya tonu a Ranar Litinin dinnan inda aka gano cewa ashe lanbo ta ke yi kamar mai cutar haukan gaske bayan tayi sama da shekaru 9 tana wannan aiki.

Binciken da aka soma ya nuna cewa Folake Folade ba mahaukaciya bace kuma ta kan fito kamar karuwa mai zaman kan ta domin jawo maza. Kusan a haka ne wannan Baiwar Allah ta ke yin ram da mazaje tana cire sashen jikin su.

Haka zalika an bayyana cewa wannan Baiwar Allah ta kan sai dawa jama’a bangarorin jikin mutun a cikin dare a kasan gadar da ta ke zama. Manyan mutane na zuwa ta saida masu sassan jikin mutum a cikin mota ba tare da jama’a sun ankara ba

Wasu na zuwa ne da niyyar kwanciya da wannan mata, da zarar ta taba mutum dai sai ya rasa hayyacin sa, a  haka ne ta ke yin abin da ta ga dama da su har ta saidawa manyan mutane bangarorin jikin su kafin Allah ya sa dubun ta su cika

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *