Ronaldo na kara tunzura Jubentus Ta Nemi Marcelo

Ronaldo na kara tunzura Jubentus Ta Nemi Marcelo

Daga Aliyu Mustapha

Sabon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Jubentus, Cristiano Ronaldo yanason kungiyar tayi kokari wajen ganin ta siyo dan wasan baya na gefe na Real Madrid, Marcelo domin yanajin dadin buga wasa dashi.

Marcelo ya shafe shekaru 11 a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid inda ya zura kwallaye 33 cikin wasanni 455 daya buga kuma ya lashe kofuna da dama a kungiyar ciki har da kofin zakarun turai guda hudu.

Sai dai kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid bata da niyyar siyar da dan wasan a yanzu bayan da take ganin bazata saki manyan ‘yan wasa guda biyu ba a lokaci daya kuma bata siyi wanda zai maye mata gurbinsa ba.

Sai dai ana ganin Jubentus za ta taya dan wasan a kakar wasa mai kamawa idan har dan wasan ya nuna yanason barin kungiyar kuma tuni aka bayyana cewa dan wasan yanason ya sake buga wasa da Ronaldo a kungiya daya.

Saura dai kwantaragin shekaru hudu yarjejeniyar dan wasan ta kare da Real Madrid kuma izuwa yanzu dan wasan zai kai kusan fam miliyan 30 idan har Real Madrid din ta tashi siyarwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *